Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona

- Biyo bayan yin allurar rigakafin Korona, shuagaban Pakistan ya kamu da kwayar cutar ta Korona

- Hukumomi a kasar sun bayyana cewa, shugaban a yanzu haka yana killace a gidansa saboda cutar

- Rahotanni daga kasar na bayyana cewa, kwayar cutar Korona a kara kamari a kasar ta Pakistan

Hukumomi a Pakistan sun ce gwaji ya tabbatar da Firaministan kasar Imran Khan ya kamu da korona – kwana biyu kenan bayan ya yi allurar rigakafin ta korona.

Yanzu haka ya killace kansa a gida, BBC Hausa ta ruwaito.

Mista Khan wanda yanzu shekarunsa 68 ya halarci wani taron jama’a a kwanakin da suka gabata.

KU KARANTA: Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona

Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona
Bayan yin rigakafin Korona da kwana 2, Firaminista ya kamu da Korona Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yawan masu kamuwa da korona na karuwa a Pakistan yayin da cutar ta sake yin kamari karo na uku.

Shugaban kasar Najeriya kuwa, yanzu kusan mako biyu kenan da karbar allurar ta Korona, kuma har yanzu babu wani labari mai nuna lafiya daga shugaban.

KU KARANTA: 'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki

A wani labarin daban, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta roka, maimakon tilasta wa kowa ya yi allurar rigakafin Korona ta Oxford AstraZeneca, a cewar Olorunnibe Mamora, Karamin Ministan Lafiya, Premium Times ta ruwaito.

Mista Mamora ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a garin Asaba, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) dake Asaba.

Bayanin nasa ya biyo bayan tambayar da wani dan jarida yayi ne kan dalilin da yasa har yanzu jihar Kogi bata karbi rabonta na allurar ba yayin da mafi yawan jihohin tarayya tuni sun karbi nasu kason.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel