Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona

Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona

- Karamin ministan kwadago a Najeriya ya bayyana cewa, za a fara biyan matasa kudin tallafi

- Ministan ya bayyana kudurin gwamnatin Buhari na tallafawa matasa don rage radadin Korona

- Ministan ya tabbatar da cewa, nan kusa za a fara biyan matasan kudin ta asusun bakunansu

Ma’aikatar kwadago da ayyukan yi ta Najeriya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin fitar da makudan kudi domin soma biyan 'yan Najeriya 774,000 da suka yi rijistar shirin SPW na tallafin korona.

Karamin ministan kwadago Festus Keyamo ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter,

KU KARANTA: 'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki

Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona
Albishir matasa: Shugaba Buhari zai fara tallafawa matasa don rage radadin Korona Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce nan ba dadewa ba wadanda suka yi rijistar shirin za su fara jin kararrawa a asusunsu na banki mai nuna alamun tallafin ya shigo.

Kuma a cewarsa, za a yi amfani da lambar BVN ta banki domin kaucewa masu karba har sau biyu musamman wadanda suka yi rijista da suna biyu.

Sai dai ministan bai fadi lokacin da gwamnati za ta fara biyan wannan kudin ba.

A watan Janairu ne gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin na tallafi ga matasa 750,000 da ke zaman kashe wando yayin da rashin ayyukan yi tsakanin matasan ya yi kamari talauci kuwa ya yi katutu a cikin jama'a.

KU KARANTA: Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu

A wani labarin daban, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta roka, maimakon tilasta wa kowa ya yi allurar rigakafin Korona ta Oxford AstraZeneca, a cewar Olorunnibe Mamora, Karamin Ministan Lafiya, Premium Times ta ruwaito.

Mista Mamora ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a garin Asaba, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) dake Asaba.

Bayanin nasa ya biyo bayan tambayar da wani dan jarida yayi ne kan dalilin da yasa har yanzu jihar Kogi bata karbi rabonta na allurar ba yayin da mafi yawan jihohin tarayya tuni sun karbi nasu kason.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.