'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki

'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki

-Wani shugaban 'yan bindiga a jihar Zamfara ya bayyana yadda ya hana hako a yankunan jihar

- Ya bayyana cewa, kafin gwamnati ta hana tuni kungiyarsa ta hana hakar ma'adinai a Zamfara

- Wani kwamishina kuwa ya bayyana rashin fa'idar hana hakar ma'adinai a yankunan jihar

Wani shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Shehu Rekeb, ya ce kungiyar sa ta haramta ayyukan hakar ma’adanai a duk wuraren da su ke aiki.

Gwamnatin Tarayya ta alakanta ayyukan masu hakar ma'adanai da 'yan bindiga, kuma ta ba da umarnin dakatar da hakar ma'adanai a jihar.

Amma a zantawarsa da Daily Trust, Rekeb ya ce tun kafin umarnin na gwamnatin tarayya, kungiyar tasa ba ta barin masu hakar ma’adanai a wuraren da suke da karfi.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa mata a fadin Najeriya

'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki
'Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“A da, fararen fata su kan tafi mahakar ma'adinai tare da rakiyar jami'an tsaro amma yanzu an daina hakan.

“Mun hana… amma makiyaya ba su san yadda ake hakar ma'adinai ba. Mutanen da muke bai wa izini su ne kauyukan da suke talakawa kuma ba su da abinda zasu rayu dashi.

"Muna ba su damar shiga wasu wurare don samun abin da za su rayu da shi. Amma mun hana hakar ma’adanai,” in ji shi.

A ranar 2 ga Maris, Gwamnatin Tarayya ta ayyana Zamfara a matsayin yankin da jirgi ba zai yi zirga-zirga ba sannan kuma ta hana hakar ma'adinai.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana ra'ayin sa game da shakkun idan har matakin zai iya kawo karshen ta'addancin.

A wata tattaunawa a kwanannan, Kwamishinan Muhalli da Ingantattun Ma’adanai, Dakta Nuraddeen Isah, ya ce ayyana yankin a matsayin inda jirgi ba zai yi zirga-zirga ba, ba zai kawo canjin da ake tsammani ba game da yanayin tsaro a jihar.

KU KARANTA: Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu

A wani labarin daban, An harbe mai taimakawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Abba Abbey Gidan Haki, wanda ’yan bindiga suka sace a daren Alhamis a Sokoto.

Anyi jana'izar shi a daren Juma'a, The Nation ta ruwaito. Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Usman dan Fodiyo dake Sokoto, Sheikh Abubakar Shehu Na Liman ne ya jagoranci sallar jana’izar.

Sallar jana’izar ta samu halartar Sanata Wamakko, Ministan Harkokin ’Yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi da shugaban riko na APC na jihar Sokoto,Alhaji Isa Sadiq Achida.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel