Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba

Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba

- Karamin minsitan lafiya ya bayyana matsayar gwamnati game da allurar rigakafin Korona

- Ministan ya bayyana cewa, gwamnati bata da shirin tilastawa kowa dole sai ya yi allurar

- A cewarsa, gwamnati za ta bi hanyar wayar da kai ne domin mutane su aminta da allurar

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta roka, maimakon tilasta wa kowa ya yi allurar rigakafin Korona ta Oxford AstraZeneca, a cewar Olorunnibe Mamora, Karamin Ministan Lafiya, Premium Times ta ruwaito.

Mista Mamora ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, a garin Asaba, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) dake Asaba.

Bayanin nasa ya biyo bayan tambayar da wani dan jarida yayi ne kan dalilin da yasa har yanzu jihar Kogi bata karbi rabonta na allurar ba yayin da mafi yawan jihohin tarayya tuni sun karbi nasu kason.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa mata a fadin Najeriya

Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba
Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba Hoto: health.gov.ng
Asali: UGC

Don haka, Mista Mamora ya yi sauri ya nuna cewa jihar Kogi ba a shirye ta ke ba da allurar rigakafin, yayin da Gwamnatin Tarayya kuwa ba za ta tilasta wa kowace jiha yin allurar ba.

“Kogi ba ta da wuraren ajiyar kayan sanyi, tsaro, kayan aiki da kuma ma’aikatan da za su yi allurar rigakafin.

“Har ila yau, bari in bayyana a sarari a nan cewa tun daga farko, Gwamnatin Tarayya ta bayyana karara cewa ba za ta tilasta wa kowa ya yi rigakafin ba, a maimakon haka za ta ci gaba da yin kira ga mutane su yi don radin kansu.

“Baya ga haka, jihar Kogi, da musamman ka ambata, daya daga cikin dalilan da ya sa ba a tura allurar can ba shi ne; saboda lokacin rikicin #EndSARS, an lalata wasu cibiyoyinsu da karfin tsiya.

“Don haka, yayin da muke magana, jihar Kogi ma ba ta da wuraren adanawa don kula da yanayin sanyi. Don haka, wannan shi ne dalilin da ya sa ba a samarwa jihar ba,” inji shi.

Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ba da sharadi ga jihohi, don tabbatar da shirye-shiryen samar da kayan sanyi, kayan aiki, tsaro da ma'aikata don yin allurar rigakafin, kafin a samar da su.

KU KARANTA: Yan bindigan Zamfara: Mun haramta hakar ma'adinai a yankunan da muke aiki

A wani labarin daban, Shugaban Kwamitin Shugaban kasa (PTF) kan Korona kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da damawa da shugabannin addinai wajen wayar da kan mabiyansu game da bukatar yin rigakafin Korona.

Mista Mustapha wanda yake magana a kashi na biyu na wayar da kan malamai da limamai kan allurar da hukumar NPHCDA ta shirya a Abuja, ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa shugabannin a dukkan matakai sun yi allurar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel