Kenya ta bi sahun Najeriya, Farashin man Fetur ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar

Kenya ta bi sahun Najeriya, Farashin man Fetur ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar

- Hukumar dake kula da albarkatun man Fetur ta ƙasar Kenya (EPRA) ta kare kanta bayan maganganu sun yawaita akan tashin da farashin man Fetur ya yi a ƙasar

- Kamar dai yadda ta faru a Najeriya inda aka fuskanCI makamancin haka na tashin farashin man Fetur din a kwanakin baya

- Rahotanni daga ƙasar Kenya sun bayyana cewa farashin litar man Fetur din ya wuce Sh120.

Hukumar da ke da alhakin kula da albarkatun man Fetur na kasar Kenya (EPRA) ta kare kanta kan magan-ganun da sukayi yawa a ƙasar biyo bayan tashin gwauron zabi da litar man fetur ya yi wanda ba'a yi tsammani ba.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari wuta

Kamar dai yadda ta faru a Nijeriya, inda akai ta cece-kuce bayan tashin da farashin man fetur ya yi a kwanakin baya. farashin sai da yakai N212 a wasu sassan ƙasar ta Najeriya.

Rahotanni daga jaridun ƙasar Kenya sun bayyana cewa, farashin litar man fetur daya ya haura Sh120, wanda rabon da kasar ta fuskanci faruwar hakan shekara tara kenan.

Kenya ta bi sahun Najeriya, Farashin man petur ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar
Kenya ta bi sahun Najeriya, Farashin man petur ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar Hoto: ntvkenya
Source: Twitter

Tashin farashin dai yazo dai-dai da lokacin da 'yan ƙasar ke fama da annobar cutar COVID19 a karo na uku, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: 2023: Ana halin fargaba yayinda PDP ke shirin yanke hukunci kan yankin da za ta baiwa tikitin Shugaban kasa

Hakan ya jawo ma hukumar EPRA matsin lamba, wanda yasa ta bada umarnin duba farashin da kuma lalubo hanyar da za'a shawo kan lamarin.

EPRA ta bayyana cewa ana ƙayyade farshin man fetur a ƙasar Kenya ne ga 'yan ƙasa daidai da dokar ƙayyade farashin mai ta 2010.

A wani labari kuma Tambuwal Ya Musanta Jita-Jitar Cewa Anyi Ƙoƙarin Sace Ɗalibai A Sokoto

Gwamnan wanda ya yi saurin zuwa makarantar ya tabbatar da cewa wata 'yar hatsaniya ce tafaru amma ba kamar yadda ake yaɗawa ba.

An dai samu rikici ne a makarantar dake Dingyaɗi bayan jama'a sun biyo wani ɓarawon babur har cikin makarantar.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Source: Legit

Online view pixel