Tambuwal Ya Musanta Jita-Jitar Cewa Anyi Ƙoƙarin Sace Ɗalibai A Sokoto
- Gwamnan Sokoto ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa wasu 'yan bindiga sun yi ƙoƙarin sace ɗalibai a jihar Sokoto
- Gwamnan wanda ya yi saurin zuwa makarantar ya tabbatar da cewa wata 'yar hatsaniya ce tafaru amma ba kamar yadda ake yaɗawa ba
- An dai samu rikici ne a makarantar dake Dingyaɗi bayan jama'a sun biyo wani ɓarawon babur har cikin makarantar.
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa wata hatsaniya da ta faru a makarantar sakandiren Dingyaɗi na da alaƙa da ƙoƙarin sace ɗaliban makarantar.
KARANTA ANAN: Hukumar JAMB Ta Tuhumi Ma'aikatanta biyu Kan Badaƙalar Gurbin Shiga Jami'a
Gwamnan wanda ya yi gaggawar zuwa makarantar lokacin da yaji labarin ya bayyana ma manema labarai cewa jama'a ne suka biyo wani barawon babur wanda ya shiga cikin harabar makarantar.
Gwamnan yace: "Lamarin ya shafi wani ɓarawon babur ne da ya ruga cikin harabar makarantar ya yin da wasu gungun jama'a ke biye da dashi."
"Sai dai, Shigar jama'a harabar makarantar babu zato ba tsammani ya tsoratar da ɗaliban makarantar har wasun daga cikin su suka fara kiran iyayen su domin a zaton su wasu ne suka zo su tafi da su." inji gwamnan.
Bayan haka, gwamnan ya yi jawabi ga ɗaliban kuma ya tabbatar musu da cewa gwamnatin sa na nan akan bakarta na tabbatar da tsaro ta kowane hali.
KARANTA ANAN: Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024
Ya kuma yi kira ga al'ummar yankin da kada su damu, su cigaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tanbuwal ya ƙara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar da kuma sauran hukumomin tsaro zasu yi bincike akan lamarin.
A wani labarin kuma An kama tsohon dan gidan fursuna da aka yi wa rangwame yana siyar da miyagun makamai ga 'yan ta'adda.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wata kungiyar masu safarar miyagun makamai.
Daga cikin wadanda ake zargin kuma aka kama, akwai wani mai suna Anthony Base, wanda aka kama, aka gurfanar sannan aka kai shi gidan yari saboda wannan laifin amma sai wani gwamnan arewa maso yamma yayi masa rangwame aka sako shi.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng