Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari wuta

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari wuta

Wasu tsagerun yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, wuta.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kai wa motocin sarkin hari ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari da yammacin ranar Talata.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya gana da Sarakunan gargajiyan jihar ranar Talata.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa Sarkin bai cikin motar lokacin da harin ya auku.

Direban Sarkin, Umar Jibril, ya bayyana cewa sarkin na wani wuri lokacin.

A hirarsa da Daily Trust, ya ce yan bindigan sun budewa motocin wuta kuma shine a gaba amma Allah ya kiyayeshi.

"Bamu tsaya ba, sun harbo min bindiga amma cikin ikon Allah harsashin bai same ni a kai ba," yace.

Ya ce sabanin kananan raunuka da suka samu, babu wanda ya jigata.

Birnin Gwari na cikin kananan hukumomin jihar Kaduna da yan bindiga suka addaba.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari wuta
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sarkin Birnin Gwari wuta
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel