Dole Ne Mu Shirya Fuskantar Kalubale A Zaben 2023, Inji Shugaban Matasan APC

Dole Ne Mu Shirya Fuskantar Kalubale A Zaben 2023, Inji Shugaban Matasan APC

- Shugaban matasan jam'iyyar APC ya bayyana cewa akwai babban ƙalubale a gaban jam'iyyarsu idan suna son zarcewa a zaɓe mai zuwa

- Ya bayyana haka ne a sa'ilin da yake jawabi ga shuwagabannin jam'iyyar na ƙananan hukumoni 27 a Jigawa.

- Isma'il Ahmed yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da ikon takara a zabe mai zuwa, rashin sa kadai babban kalubale ne.

Shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Ismail Ahmed, ya gargadi 'yan jam'iyyar da su shirya fuskantar kalubale mai girma a babban zaben dake tafe.

Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam-iyyar daga kananan hukumomi 27 na jihar Jigawa jiya a Dutse, a wani bangare na cigaba da shirin wayar da kai na jamiyyar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami

Isma'il yace: "A dalilin rashin babban dan takara kamar shugaba Muhammadu Buhari a zabe dole ne sai jam'iyyar ta zage damtse."

"Tunda shugaba Buhari bai da hurumin kara tsayawa takarar shugaban kasa, akwai bukatar jam'iyya ta samar da hadadden shiri wanda zai bata nasarar lashe zabe." a cewarsa.

Dole Ne Mu Shirya Fuskantar Kalubale A Zaben 2023, Inji Shugaban Matasan APC
Dole Ne Mu Shirya Fuskantar Kalubale A Zaben 2023, Inji Shugaban Matasan APC Hoto:@Apcyouthforum1
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa shugaban rikon kwarya na jam'iyyar ya shirya tsaf don ganin jam'iyya ta ba kowane ɗan ta damar neman dukkanin kujerar da yake muradi.

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023: Wani ɗan majalisa ya roƙi gwamnan Rivers Wike ya fito takarar shugaban ƙasa

Ya bayyana matasa da mata a matsayin wani babban jigon jamiyyar, ya lura da cewa makasudin shirin wayar dakan shine nemo wajajen da suke da matsaloli da zummar samar da hanyoyin magance su.

A nasa jawabin shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a jihar, Muhammadu Umar Dikkuma ya koka kan yadda matasan arewa suka zama koma baya a kasa.

A wani labarin kuma 'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m

Mutanen gari da rundunar 'yan sanda sun yi nasarar dakile yunkurin kwace kudin nasu.

Kwastoman bankin ya sha dakyar, yayin da 'yan bindigan ke harbin tayoyin motarsa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Source: Legit

Online view pixel