'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m

'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m

- Wasu 'yan fashi sun kai wa wani kwastoman banki hari domin kwace kudinsa N10m

- Mutanen gari da rundunar 'yan sanda sun yi nasarar dakile yunkurin kwace kudin nasa

- Kwastoman bankin ya sha dakyar, yayin da 'yan bindigan ke harbin tayoyin motarsa

A ranar Litinin ne wasu mazauna gari da 'yan sanda suka ceci wani abokin cinikayyar banki a jihar Bayelsa daga hannun wasu gungun 'yan fashi da makami da suka kwace masa kudi N10m, The Punch ta ruwaito.

Lamarin ya ce ya faru ne a kusa da babbar hanyar Sani Abacha da ke yankin Amarata a Yenagoa babban birnin jihar, inda wanda abin ya rutsa dashi ya ciro kudin daga wani banki.

An tattara cewa ya fito daga banki, ya shiga motarsa kuma yana kan hanyarsa ta komawa lokacin da 'yan fashin suka buge shi.

Wata shaidar gani da ido, Mary Fabi, ta ce 'yan fashin, wadanda suka bi kwastoman da Motar Sport, sun harbe shi sau da yawa amma ya ki tsayawa.

KU KARANTA: Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye

'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m
'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ta ce 'yan fashin sun kuma harbi tayoyin motar mutumin lamarin da ya tilasta motar ta tsallake zuwa wani gefen hanya kuma ta yi dungure sau biyu kafin ta buge keke napep amma ba wanda ya mutu.

Hadarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a kan titin da ke cike da mutane yayin da jama'a ke bin ‘yan fashi da makamin, daga nan suka tsere ba tare da sun karbi kudin ba.

Kokarin da 'yan sanda suka yi a bankin da kuma wadanda suka taimaka, sun hana 'yan fashi da makamin su sace kudin N10m.

An ce kwastoman da aka ceto da kuma mai keke napep an kai su wata cibiyar kiwon lafiya mafi kusa domin kulawa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Bayelsa, Asinim Butswat, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba game da lamarin fashin ba, sannan ya yi alkawarin bada bayani nan gaba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25

A wani labarin, Adadi mai yawa na rundunar 'yan ta'addan Boko Haram da na takwarorinsu ISWAP sun yi kicibus da rundunar sojojin Operation Lafiya Dole a yankin Tafkin Chadi da Tumbus.

Rahoto ya tabbatar da cewa, rundunar sojin sun kashe adadi mai yawa na 'yan ta'addan kungiyar ta Boko Haram da ISWAP.

Hadakar sojojin na sashin da ke sintiri a kan iyakar Tafkin Chadi sun ci gaba tare da share kauyukan Daban Massara da Ali Sherifti da sauran kauyukan da 'yan ta'addan suka mamaye, kafin daga bisani suka wuce gaba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel