Zaɓen 2023: Wani ɗan majalisa ya roƙi gwamnan Rivers Wike ya fito takarar shugaban ƙasa
- Wani ɗan majalisar tarayya daga jihar Kogi ya roƙi gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da ya fito takarar shugaban Ƙasa a zaɓen da ke tafe
- Dan Majalisa Tajuddeen yace gwamnan ya cancanci babban matsayi a ƙasar duba da nasarorin da ya samu a matsayin gwamna
- A cewarsa duk da matsalolin da Najeriya ke ciki amma gwamnan ya bada gudummuwa sosai wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa
Ɗan majalisar wakilai daga jihar Kogi, Yusuf Tajuddeen, ya yi kira ga gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da ya fito takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP a babban zaɓen shugaban ƙasa dake tafe.
Yusuf, me wakiltar mazaɓar Kabba-Bunu/Ijumu daga jihar Kogi, ya faɗi haka ne a wani saƙo da ya fitar ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja.
KARANTA ANAN: Jerin ƙasashen Afirka 7 da kuɗaɗensu ya fi daraja a 2021
A cewar dan majalisar, duk da irin ƙalubale da halin da ƙasar nan ke ciki, wike ya cigaba da bada kyakkyawar gudummuwa ga tattalin arziƙin ƙasar nan, PM News ta ruwaito.
A saƙon da ya fitar Tajudden yace:
"Nasarorin da gwamna Wike ya samu ya nuna cancantarsa da wani babban matsayi a Najeriya. Yadda yake kula da albarkatun ƙasa dake yankinsa, da kuma yadda yake kammala manyan ayyukan da ya ɗakko na nuni da cewa shi ne yafi cancanta ya ceto kasar nan daga halin da take ciki."
KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25
"Ayyukan da ake yi na gina ƙasa da kuma manyan aikin da gwamnan ke kula da su ne suke jawo hankulan jama'a da kuma masana harkar shugabancin ƙasar nan," inji shi.
"Wike ya bada gudummuwa a kowane ɓangaren cigaba na ƙasar nan kamar; gyara ɓangaren lafiya, Noma da kuma ilimi," a cewar Yusuf.
Yusuf ya ƙara da cewa: "Ko aikin gadajen sama da aka watsar a Patakwal ya isa ya nuna kwarewarsa da kuma cancantarsa da ya nemi wannan kujerar."
A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya shawarci mata da su yi koyi da Ngozi
Shugaban ya bayyana cewa, ya kamata mata su yi koyi da Ngozi wajen jajircewa kan aiki.
Nogozi ta godewa shugaban tare da alkawarta tallafawa Najeriya ta bangarenta a kungiyar.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano. Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng