Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami

Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami

- Jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin lemon dan tsami a fadin jihar ta Kano nan take

- Jihar ta koka kan yadda sinadarin ke haifar da wasu cututtuka da take zargin masu kisa ne

- Jihar zuwa yanzu ta kame buhunna sama 583 na sinadarin ake zargin wa'adin amfaninsun ya kare

Gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar ga jama'a.

Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25

Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami
Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami Hoto: iStock
Asali: UGC

Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.

Ya kara da cewa sakamakon binciken da suke yi sun kama buhunna 583 na irin wadannan sinadiran da wa'adinsu ya kare.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25

A wannan daban, Akalla mutum biyu sun hallaka yayinda 167 ke kwance asibiti ranar Alhamis sakamakon shan lalataccen sinadarin hada lemu a jihar Kano.

Bayan shan wannan abu, wasu cikin marasa lafiya suka fara amai da ganin jiri, hakazalika wasu suka fara fitsarin jini, rahoton Daily Nigerian. An tattaro cewa unguwannin da wannan abu ya fi shafa sun hada da Warure, Dandago da Sabon Sara.

Rahoton ya bayyana cewa a Warure Makasa, mutum 13 yan gida daya suka jigata. A Garangamawa da Sabon Sara kuwa mutum biyu sun mutu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel