Ba wani abin tsoro, rigakafin Korona ta Astrazeneca ingantacciya ce, NPHCDA

Ba wani abin tsoro, rigakafin Korona ta Astrazeneca ingantacciya ce, NPHCDA

- Hukumar lafiya ta ƙasa tace babu wani abun tsoro a rigakafin Astrazeneca saboda hukumar lafiya ta duniya ta amince da ita.

- Shugaban NPHCDA, Dr. Faisal Shu'aib ne ya bayyana haka don martani ga jita-jitar da wasu ke yi cewa allurar ba ingantacciya bace.

- Ya ce hukumar sa na aiki kafada-da-kafada da hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi ta kasa (NAFDAC).

Shugaban hukumar lafiya ta kasa, Dr, Faisal Shu'aib, ya bayyana cewa rigakafin Astrazeneca ta samu amincewar hukumar lafiya ta duniya (WHO) da kuma hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi ta ƙasa (NAFDAC).

Shu'aib ya kara da cewa kasancewar rigakafin bata jure yanayi mai zafi, bashi ke nuna bata da inganci ba, kamar yadda PM News ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ya shawarci mata da su yi koyi da Ngozi Okonjo-Iwela

"Muna aiki kafada-da-kafada da NAFDAC domin duba duk wani canji da allurar ka iya yi" a cewarsa.

Ya kara da cewa: "Bayan matakan da muka dauka tun kafin mu raba alluarar, NAFDAC ta kirkiro da wata manhaja 'safety app' saboda mutane su sauke a wayoyin su."

"Ina san ina tabbatar ma da yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya da kwamitin yaƙi da cutar COVID19 sun shirya tsaf don ganin an gudanar da wannan rigakafin a faɗin kasar," inji Faisal.

Ba wani abin tsoro, rigakafin Korona ta Astrazeneca ingantacciya ce, NPHCDA
Ba wani abin tsoro, rigakafin Korona ta Astrazeneca ingantacciya ce, NPHCDA Hoto: @NphcdaNG
Source: Twitter

"Yana da kyau ma mutane su gane, babu wata hukuma da ta amince da wannan rigakafin da take ba'a yarda da ita ba. Kawai dai rigakafin Astrazeneca ba ta da juriyar yanayi kamar na sauran rigakafin COVID19," Faisal ya faɗa.

KARANTA ANAN: Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

"Kamar yadda muka sani an fara amfani da rigakafin Astrazeneca a sassa daban-daban na duniya. Duk da cewa wasu kasashen turai sun dakatar da amfani da rigakafin saboda wani abu da ya taso, WHO tare da kwamitin ta na rigakafi sun bayyana cewa babu wani dalili da zaisa a dena amfani da rigakafin Astrazeneca,".

"Hakanan kuma, Burtaniya tace babu wata kwakkwarar hujja da take nuna rigakafin na haifar da cutar jini," inji Faisal.

NAN ta ruwaito cewa, a wani sako da NPHCDA ta fitar ranar 11 ga watan Maris, ya bayyana cewa hukumar zata cigaba da bibiyar cigaban dake wakana a kashin rigakafin "ABV5300."

A wani labari kuma 'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25.

Rahotanni sun ce, 'yan bindigan sun bukaci a biya kudin fansa sama da Naira miliyan 50.

'Yan bindigan sun yi kashedin kashe mafarautan matukar ba a biya kudin fansan ba nan take.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Source: Legit

Online view pixel