Shugaba Buhari ya shawarci mata da su yi koyi da Ngozi Okonjo-Iwela
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Ngozi Okonjo-Iwela a fadarsa a yau Litinin
- Shugaban ya bayyana cewa, ya kamata mata su yi koyi da Ngozi wajen jajircewa kan aiki
- Nogozi ta godewa shugaban tare da alkawarta tallafawa Najeriya ta bangarenta a kungiyar
Shugaban kasar Najeriya, Manjo-Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya karbi bakwancin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala a fadarsa da ke Abuja, BBC Hausa ta ruwaito.
A ganawarsu, shugaba Muhammadu Buhari ya shaida cewa duk da cewa Najeriya ta goyi-bayanta wajen nasararta, yana kuma alfahari da matakin da ta kai a rayuwarta.
Sanawar da mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce Buhari yana alfahari da Dokta Okonjo-Iweala domin ta karawa Najeriya martaba da daraja a idon duniya, kuma yana fatan sauran mata a kasar za su yi koyi da ita.
KU KARANTA: Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3
Sannan ya ce gwamnati za ta yi kokari wajen sake karfafawa matasa domin fuskantar manyan kalubale na rayuwa nan gaba.
A nata martanin Mrs Okonjo-Iweala ta godewa Najeriya da fadar gwamnati Buhari da matasa bisa soyayya da goyon-bayan da ta samu.
Sannan ta alkawarta bude kafofi da taimakawa Najeriya ta kungiyar da take jagoranta wajen ciyar da kasar gaba.
A ranar 1 ga watan Maris, Mrs Okonjo-Iweala ta kama aiki a matsayin mace ta farko kuma bakar-fata da ke rike shugabancin kungiyar ta WTO.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Wasu daliban firamare da aka sace a Kaduna sun tsare daga hannun 'yan bindiga
A wani labarin daban, Farfesa Chukuka Okonjo, mahaifin darakta janar ta cibiyar kasuwanci ta duniya, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, ya rasu.
Daily Trust ta wallafa cewa, a wata takarda da darakta janar ta WTO, a mamadin iyalan ta fitar a ranar Litinin, tace Obi na Ogwashi-Uku da jihar Delta ya rasu yana da shekaru 91 a duniya.
"A madadin 'yan uwana na gidan sarautar Umu Obi Obahai, ina sanar da mutuwar mahaifina, Obi Farfesa Chukuka Okonjo, tsohon Obi na Ogwashi-Uku. Dan jihar Deltan ya rasu yana da shekaru 91.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng