'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25

'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25

- 'Yan bindiga sun sace wasu mafarauta 25 tare da budewa 17 wuta suka hallakasu har lahira

- Rahotanni sun ce, 'yan bindigan sun bukaci a biya kudin fansa sama da Naira miliyan 50

- 'Yan bindigan sun yi kashedin kashe mafarautan matukar ba a biya kudin fansan ba nan take

Akalla mafarauta 17 aka kashe yayin da wasu 25 aka sace su, yayin harin wasu ‘yan bindiga da ke barna a dajin Tsayau da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Daya daga cikin mafarautan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.

"Mun tabbatar da cewa an kashe 17… wasu daga cikin mutanen da suka je neman 'yan uwansu sun shaida mana cewa sun ga gawawwaki 17," in ji shi.

Daily Trust ta tattaro cewa mafarautan sun shiga maboyar ‘yan bindigan bisa kuskure yayin farauta.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya shawarci mata da su yi koyi da Ngozi Okonjo-Iwela

'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25
'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25 Hoto: Daily Trust
Source: Twitter

'Yan fashin sun fatattake su, sun kashe mutane 17 nan take kuma suka tafi da wasu 25.

Majiyar ta ce wadanda suka yi garkuwar sun nemi a ba su kudin fansa na Naira miliyan 50 amma da aka ce ba za a iya tara irin wannan kudin ba, sai suka ce su je ga gwamnati su karba.

Ya ce daga cikin gawarwaki 17, an binne daya a can saboda gawar ta rube a kusa da mafakar 'yan bindigan.

“Muna kira ga gwamnati da ta taimaka mana wajen kubutar da mafarautan. A ranar Lahadi da yamma, sun kira sun ce idan ba a biya bukatar su ba, za su kashe su,” majiyar ta roka.

An ce mafarautan sun fito ne daga garuruwa daban-daban, ciki har da Katsina, Tsagero, Abukur, Kanyar Uban Daba, Mashi, Fadi Gurje, Ku Tare Dandagoro, Muduru da kauyukan karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Lokacin da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, ya ce akwai rahotanni masu karo da juna kan lamarin.

Katsina na daya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke addabar mazauna yankin.

KU KARANTA: Atiku ya sake jan hankalin gwamnatin Buhari biyo bayan sace dalibai a Kaduna

A wani labarin, Adadi mai yawa na rundunar 'yan ta'addan Boko Haram da na takwarorinsu ISWAP sun yi kicibus da rundunar sojojin Operation Lafiya Dole a yankin Tafkin Chadi da Tumbus.

Rahoto ya tabbatar da cewa, rundunar sojin sun kashe adadi mai yawa na 'yan ta'addan kungiyar ta Boko Haram da ISWAP.

Hadakar sojojin na sashin da ke sintiri a kan iyakar Tafkin Chadi sun ci gaba tare da share kauyukan Daban Massara da Ali Sherifti da sauran kauyukan da 'yan ta'addan suka mamaye, kafin daga bisani suka wuce gaba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel