Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

- 'Yan Boko Haram su sace wasu makiyaya, sun sheke 22 tare da yin awon gaba da shanunsu

- Kamar yadda aka tattaro, lamarin ya faru ne a cikin ranakun karshen makon da ya gabata

- 'Yan ta'addan suna kashe manoma da makiyaya saboda suna zarginsu da kaiwa sojoji bayani

Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun yi garkuwa da wasu makiyaya tare da yin awon gaba da shanunsu.

Hakazalika, 'yan Boko Haram sun kashe makiyaya 22 a jihar Borno.

SaharaReporters ta tattaro cewa an kashe makiyayan ne a ranakun karshen makon da ya gabata a Monguno.

Mai bada shawara na musamman kan tsaron kasa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babagana Monguno daga Monguno yake.

KU KARANTA: Yari ga Matawalle: Kayi taka-tsan-tsan da yadda kake kula da tsaron jihar Zamfara

Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno
Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: Facebook

Wani mazaunin garin ya sanar da SaharaReporters cewa mayakan ta'addancin sun yi garkuwa da wasu makiyaya kuma sun yi awon gaba da shanunsu.

"Mun samo gawawwakin makiyaya 22 wadanda mayakan ta'addanci na Boko Haram suka halaka," yace.

A kodayaushe mayakan ta'addancin na cigaba da harar manoma da makiyaya inda suke zarginsu da leken asiri kuma suna kaiwa sojin Najeriya bayanan sirri.

Suna cigaba da kai samame ga yankunan makiyaya tare da satar shanu inda suke amfani da kudin da suke siyar dashi don miyagun ayyukansu.

A watan Disamban 2020, 'yan ta'addan sun kutsa gonar shinkafa dake Zabarmari a karamar hukumar Jere inda suka kashe manona 43.

KU KARANTA: NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya

A wani labari na daban, Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar nan da wa'adin da yake basu tare da jan kunne.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam'iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

A ranar Juma'a ne jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kutsa kwalejin harkar noma da gandun dabbobi dake Kaduna suka kwashe dalibai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel