Har wane tsawon lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin? Atiku ya koka da satar ɗalibai mata a Arewa

Har wane tsawon lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin? Atiku ya koka da satar ɗalibai mata a Arewa

- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya koka akan satar ɗalibai mata dake ƙara yawaita a arewacin Najeriya

- Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata yace har wane lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin.

- A baya-bayannan dai an yi awon gaba da ɗaruruwan ɗalibai mata a jihar Kaduna

Tsohon shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya jajantawa iyalan ɗalibai mata da aka sace a kwalejin zamanantar da gandun daji dake Afaka, unguwar Mando ta jihar Kaduna.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: An ceto kimanin dalibai 180 cikin wadanda aka sace a jihar Kaduna

Satar ɗaliban a Kaduna yazo bayan sati biyu da kuɓutar da ɗalibai mata 300 da aka sace a makarantar sakandiren mata ta gwamnati dake garin Jangeɓe, jihar Niger, wanda wasu 'yan bindiga suka yi gaba dasu daga makarantarsu.

A shekarar 2014, Najeriya ta samu irin wannan matsalar, inda 'yan ta'addan Boko Haram suka sace ɗalibai mata sama da 200 a garin Chibok, dake jihar Borno.

Har wane tsawon lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin? Atiku ya koka da satar ɗalibai mata a Arewa
Har wane tsawon lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin? Atiku ya koka da satar ɗalibai mata a Arewa Hoto: @atiku
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Muna sake jaddadawa, ba za'a kara farashin litan man fetur ba a watan nan, NNPC

Haka zalika a shekarar 2018, Boko Haram ta sake yin awon gaba da ɗalibai mata 110 a makarantar gwamnati dake Dapchi, jihar Yobe.

Da yake magana akan lamarin a shafinsa na kafar sada zumuntar twitter, Atiku yace:

"Abun damuwa ne matuƙa a wannan yanayi da muke ciki, wanda kullum ake harin sace ɗalibai mata a yankin Arewa."

"Addu'a ta na tare da iyalan waɗanda abun ya shafa, kuma ina fatan babu wasu kuɗaɗe da za'a biya don ceto waɗannan yara." Inji tsohon shugaban ƙasan.

Atiku Abubakar ya ƙara da cewa: "Babban abin tambayan anan shine; har wane lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin?"

A wani labarin kuma Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu

Wasu jami'an 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu a jihar Kwara ranar Alhamis.

Hatsarin ya faru ne a yankin Eyenkorin, na babban birnin jihar, Illori, akan babbar hanyar Ilorin-Ogbomoso.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Source: Legit.ng

Online view pixel