Yanzu-yanzu: An ceto kimanin dalibai 180 cikin wadanda aka sace a jihar Kaduna

Yanzu-yanzu: An ceto kimanin dalibai 180 cikin wadanda aka sace a jihar Kaduna

Jami'an tsaro sun ceto dalibai kimanin 180 a cikin wadanda aka sace a kwalejin zamanantar da gandun daji dake Afaka, unguwar Mando ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan inda yace ana kokarin ceto sauran.

Aruwan ya bayyana yadda yan bindigan suka kutsa cikin makarantan cikin dare sukayi awon gaba da daliban.

"An ceto dalibai 180, har yanzu akwai wadanda ake nema sakamakon harin da aka kai makarantar zamanantar da gandun daji Afaka, karamar hukumar Igabi," Aruwan ya bayyana a jawabi.

"Jami'an Sojojin Najeriya da safiyar yau, Juma'a 12 ga watan Maris, 2021 sun ceto mutum 180, yawancinsu dalibai."

"Yan bindigan da yawansu sun kai hari makarantar misalin karfe 11:30 na daren Alhamis kuma suka kwashe dalibai da ma'aikata."

"Yan bindigan sun fasa katangan dake zagaye da makarantar inda suka kai harinsu na farko."

"Ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta samu labari kuma ta sanar da rundunar 1Div da barikin horon mayakan sama."

"Ba tare da bata lokaci ba sojin suka shiga makarantar kuma suka bude musu wuta."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng