Muna sake jaddadawa, ba za'a kara farashin litan man fetur ba a watan nan, NNPC
- Kamfanin NNPC ya yi fashin baki kan rahotannin kara farashin man fetur
- Hankulan yan Najeriya sun tashi yayinda suka wayi gari da labarin tashin farashin
- Da wuri NNPC ya aika sakon kar ta kwana don kwantar da hankulan yan Najeriya
Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya sake jaddada cewa ba za a kara farashin litan man fetur a watan Maris ba duk da tashin da farashin danyen man yayi a kasuwar duniya.
Wannan ya biyo bayana rahoton hukumar sanya farashi da kasuwanci mai a Najeriya PPPRA wanda yayi hasashen cewa farashin mai a yanzu na iya tashin N212 ga lita.
A sakon kar ta kwana da NNPC ya aike, yace: "NNPC na jaddada cewa babu kari a farashin man fetur na Ex-Depot a watan Maris."
KARANTA WANNAN: Kotun koli ta rage adadin zaman Kurkukun Joshua Dariye da shekaru 2, yanzu zai yi 10
DUBA NAN: Alhaji Dantata zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama
Hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan arzikin mai a Najeriya, ta yi lissafin yadda farashin litar PMS wanda aka fi sani da man fetur ya kamata ya kasance.
Hukumar ta bayyana wannan karin kudi ne a ranar 12 ga watan Maris, 2021 a shafinta na yanar gizo.
An yi lissafin ne a kan yadda ake shigo da kaya.
Wannan sauya-sauye da aka samu ya na nufin cewa litar fetur zai kara kudi a gidan mai. Idan aka tara duka wadannan kudi, za a saida fetur a gidan mai a kan N212.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng