Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu

Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu

- Jami'an yan sanda guda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu a jihar Kwara

- 'Yan sandan suna kan hanyar su ta dawowa babban birnin jihar, Ilori

- Jami'i mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace suna kan hanyarsu ta dawowa daga rakiyar wata mota ne lamarin ya ritsa da motar da suke ciki

Wasu jami'an 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu a jihar Kwara ranar Alhamis.

Hatsarin ya faru ne a yankin Eyenkorin, na babban birnin jihar, Illori, akan babbar hanyar Ilorin-Ogbomoso.

KARANTA ANAN: 'Yan bindiga sun halaka mutum 7 a Kaduna, sun kone gidaje da dama

Sauran mutanen da lamarin ya sahafa sunji munanan raunika.

'Yan sandan sun raka wata mota ne zuwa Ogbomoso, daga Ilori, saidai a hanyar su ta dawowa ne sukayi taho mugama da wata babbar mota.

Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu
Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu a wani mummunan hatsari da ya ritsa dasu Hoto: @policeNG
Asali: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa an kai gawar mamatan zuwa Asibitin koyarwa na jami'ar Ilori, sannan kuma waɗanda suka jikkata suna amsar kulawa ta musamman a asibitin.

KARANTA ANAN: Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N- Power

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace:

"Jami'an 'yan sandan nakan hanyar su ta dawowa daga garin Ogbomoso bayan sun raka wata mota. Tayar ɗaya daga cikin motocin ta fashe wanda hakan ya yi sanadiyar hatsarin tare da wata babbar motar ɗaukan kaya."

"Nan take biyu daga cikin 'yan sandan sukace ga garinku nan, wasu kuma suka jikkata, yanzun haka suna karɓar magani a asibiti," a cewarsa.

Shugaban hukumar kare haɗurra ta kasa reshen jihar ya tabbatar da faruwar hatsarin.

A wani labarin kuma Buhari Ya Ƙaddamar Da Sabon Ginin Hukumar Raya Yankin Niger-Delta

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit.ng kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262