Labari mai zafi: Gwamnati ta buga sabon lissafi, za a koma saida litar man fetur a kan N212

Labari mai zafi: Gwamnati ta buga sabon lissafi, za a koma saida litar man fetur a kan N212

- PPPRA ta fitar da kudin da ake kashewa wurin shigo da mai Najeriya

- Hukumar ta tabbatar da cewa litar man fetur ya na tashi a kan N212.1

- Idan ba a dawo da tallafin fetur ba, farashi zai tashi sosai a gidajen mai

Hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan arzikin mai a Najeriya, ta tsaida farashin litar PMS wanda aka fi sani da man fetur a kan N212.11.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yi wannan karin kudi ne a ranar 12 ga watan Maris, 2021.

PPPRA ta bada wannan sanarwa ne a jeringiyar farashin kayan mai da ta fitar a wannan watan na Maris. An yi lissafin ne a kan yadda ake shigo da kaya.

Ma’ikatar NPA mai kula da tasoshin ruwa ta na karbar N2.49 a kan kowane lita, bayan haka NIMASA mai lura da hanyoyin ruwan kasar ta na cin N0.23.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin litar man fetur zuwa N100

Ana kuma karbar N1.61 a matsayin ladar ajiyan gangunan mai, bayan N2.17 da ake karba a matsayin haraji na kowace litar man fetur da ta shigo kasar.

Idan aka yi lissafi, kowace litar fetur da aka tace, za ta tashi a kan N189.61 kafin ta iso kasar nan.

PPPRA ta tsaida kudin sari a kan N4.03, gwamnati za ta karbi N1.23 a matsayin gudunar wa, sai kuma kudin dako watau na jigilar man fetur ya tashi a N3.89.

Akwai sauran kudi kamar na MTA da na karaso da mai da za a rika karbar kusan N8 a kan kowace litar man fetur kamar dai yadda hukumar PPPRA ta sanar.

KU KARANTA: NNPC ta rage wa dillalan kudin man fetur a Najeriya

Labari mai zafi: Gwamnati ta buga lissafin a koma saida litar man fetur a kan N212
Gidan mai Hoto: nigeria.total.com
Asali: UGC

Wannan sauya-sauye da aka samu ya na nufin cewa litar fetur zai kara kudi a gidan mai. Idan aka tara duka wadannan kudi, za a saida fetur a gidan mai a kan N212.

Tun kwanaki kun ji labari cewa danyen mai ya tashi a kasuwa, shiyasa aka fara tunanin cewa farashin litar man fetur zai iya kai wa tsakanin N185-N200 a Najeriya.

‘Yan kasuwa sun bayyana cewa a yadda kasuwar Duniya ta ke a yanzu, ya kamata farashin PMS watau man fetur ya tashi, idan ba dai za a sake shigo da tsarin tallafi ba.

A karshen Disamban 202, ana saida danyen man ‘Brent’ a kan $51.22, kuma gwamnati ta yi ragin N5 a kan lita. Kawo yanzu gangar danyen man mu na gida ya kai $70.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel