Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin man fetur zuwa N100 a kowace lita

Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin man fetur zuwa N100 a kowace lita

- Gwamnatin Najeriya ta bayyana kudurin rage farashin man fetur zuwa kasa da N100 a lita

- Akwai yiyuwar rage farashin bayan wani zama da gwamnatin kasar zata yi kan lamarin

- Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta ne ya bayyana hakan

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rage farashin mai zuwa N100 kan kowace lita, Vanguard News ta ruwaito.

A cewar Enang, gwamnatin tarayya ta kuma kammala shirye-shiryenta na gudanar da taron kasa kan hada aikin matatar mai ta zamani domin inganta karfin aikin da kuma rage farashin albarkatun mai.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata a Abuja.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona

Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin man fetur zuwa N100 a kowace lita
Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin man fetur zuwa N100 a kowace lita Hoto: Business Day
Asali: UGC

Tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa, Fadar Shugaban Kasa za ta gudanar da taron a ranakun 16 da 17 ga Maris.

Mista Enang ya lura cewa sakamakon taron zai taimaka wajen karya farashin kasar na albarkatun mai.

A cewarsa, taron zai tattara duk wata kadara ta Najeriya, da suka hada da masu fasaha, injiniyoyi, da sauran fannonin da suka dace, gami da wadanda ke samar da albarkatun mai a kasar.

“Kamar yadda farashin danyen yake hau-hawa , farashin matatun mai ya tashi sama, amma idan muka tace wadannan kayan man a Najeriya, kudin zai yi kasa sosai.

"Manufar taron ita ce tattara wadannan albarkatun ta yadda za mu iya kawo farashin mai da aka tace zuwa kasa da N100 a kowace lita. ”

KU KARANTA: Tuban muzuru 'yan bindiga ke yi su karbi kudinmu su siya makamai, gwamnan Neja

A wani labarin, Jaridar CNBCTV ta rahoto cewa gangar danyen man fetur ya yi tashin da bai taba yi ba a kasuwannin Duniya a wannan shekarar ta 2021.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a karon farko a 2021, gangar danyen fetur ya haura $70. Abin da ake saida gangar danyen mai a kasuwar Duniya a yau shi ne $71.28.

A kudinmu na gida, farashin gangar danyen zai kai kusan N30, 000. Hakan na zuwa ne bayan kungiyar OPEC ta kasashen da ke da arzikin mai ta ki bada dama a kara adadin danyen man da za a rika hako wa a kullum.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.