Danyen mai ya tashi a kasuwa, farashin litar man fetur zai iya kai wa N185-N200

Danyen mai ya tashi a kasuwa, farashin litar man fetur zai iya kai wa N185-N200

- Yan kasuwa suna ganin cewa ya kamata litar mai ta kai N200 a yau

- A halin yanzu ana saida fetur ne tsakanin N160-N165 a gidajen mai

- Amma kuma danyen mai ya na ta kara tsada a kasuwannin Duniya

‘Yan kasuwa sun bayyana cewa a yadda kasuwar Duniya ta ke a yanzu, ya kamata farashin PMS watau man fetur ya tashi, idan ba a shigo da tallafi ba.

A ranar Litinin, 8 ga Fubrairu, 2021, Punch ta rahoto ‘yan kasuwa su na cewa ya kamata litar man fetur ya rika tashi a kan N185 zuwa N200 a gidajen mai.

Hakan na zuwa ne bayan danyen mai ya kara kudi a kasuwar Duniya, musamman a makon jiya, amma watanni biyu kenan farashin lita bai canza a gida ba.

Wasu manyan kungiyoyin ‘yan kasuwa sun yi magana da jaridar, inda su kace wannan karin farashin danyen mai ya sa gwamnati ta dawo da kudin tallafi.

KU KARANTA: Za a ga sauyi a farashin fetur - Minista

A karshen Disamban bara, ana saida danyen man ‘Brent’ a kan $51.22, kuma gwamnati ta yi ragin N5 a kan lita. Kawo yanzu danyen man kasar ya kara kudi.

Daga karin litar fetur da aka yi Nuwamban 2020 zuwa yanzu, gangar danyen man Najeriya ya tashi da 43% a kasuwa; daga $41.51 a lokacin zuwa $59.34 a yau.

A cewar wadannan ‘yan kasuwa, litar man da ake saida wa tsakanin N160 zuwa N165 a gidajen mai a Najeriya, ya kamata yanzu ya kai akalla N185 zuwa N200.

Shugaban wata kungiyar ‘yan kasuwa, Mista Clement Isong, ya ce: “Ya danganta da canjin kudi, amma ya kamata kudin lita ya tsaya ne tsakanin N185 da N200.”

KU KARANTA: Ana satar danyen mai - Majalisa

Ya kamata ace ana saida mai a kan N185 zuwa N200 inji ‘Yan kasuwa
Shugaba Buhari ya na jawabi Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Idan har za a cigaba da saida mai a kan yadda mu ke saida wa, to wani ya na daukar nauyin tallafi, kuma gwamnati ba za ta iya biyan wannan kudi a yanzu ba.”

Kamfanin NNPC ta bakin kakakinta, Dr. Kennie Obateru ta musanya batun dawo da tallafin man fetur

A makon nan kun ji cewa Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya za ta zauna a kan rahoton farashin wuta da fetur.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta koma tebur da kungiyoyin kwadago a ranar 22 ga watan Fubrairu, 2021 kan maganar farashin litar man fetur da kudin lantarki.

Hakan na zuwa ne bayan Chris Ngige da wakilan gwamnatin tarayya sun yi zama da kungiyoyin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel