NNPC ta rage wa dillalan kudin man fetur zuwa N108
Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, a daren ranar Laraba ya sanar da cewa ya rage farashin lita man fetur da ya ke sayarwa dillalan mai daga N113.28 zuwa N108.
Wannan na cikin wata sanarwa ne da mai magana da yawun kamfanin, Dr Kenny Obateru ya fitar a Abuja a ranar Laraba.
Ya ce rangwamen da aka yi ya fara aiki a dukkan rassan sa da wuraren da ya ke kasuwanci kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Dr Kennie Obateru, ya ce ya jiyo Manajan kamfanin, Musa Lawan, yana cewa rangwamen da aka yi a farashin lita man fetur na daga cikin sabbin tsare tsaren kasuwanci na kamfanin.
DUBA WANNAN: Katsina: An yanke wa dattijo dan shekara 70 da ya zazzagi Buhari hukunci
Lawan ya ce an dauki wannan matakin ne domin bunkasa ciniki tare da kuma bin dokokin farashi da mahukunta suka gindaya.
Ya yi bayanin cewa sabon farashin zai bunkasa ciniki ta yadda kamfanin za ta sayar da dimbin biliyoyin litar mai da ke maajiyar ta tare da samar da abokan huldar ta man fetur a farashi mai rahusa.
Lawan ya ce an cimma wannan matsayar ne bayan yin nazari a kan halin da ake ciki game da farashin man fetur da kamfanin ya yi.
Sai dai kamfanin ba ta bayyana ko wannan rangwamen da aka yi wa dilalai yana nufin za a rage wa alumma farashin litan man fetur ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng