Anyi ma Gwamna Ganduje Allurar rigakafin Korona A Asibitin Murtala dake Kano

Anyi ma Gwamna Ganduje Allurar rigakafin Korona A Asibitin Murtala dake Kano

- Anyi ma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje rigakafin korona yau.

- Gwamnan ya yi kira ga al'ummar jihar da su bada haɗin kai ga jami'an lafiya don ayi musu rigakafin

- Kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana jin dadinsa da irin kyakkyawar gudummuwa da gwamnan ke bayarwa wajen yaƙi da cutar.

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi allurar rigakafin korona a asibitin Murtala dake birnin Kano a yau Alhamis.

Likitan gwamnan ne ya yi masa rigakafin ta Astrazeneca a gaban wasu daga cikin jami'an gwamnatin jihar, wakilan Masarautar jihar da kuma wasu jami'an lafiya.

KARANTA ANAN: Abdulsalami da matarsa sun yi allurar riga-kafin COVID-19 a Minna

Kafin ayi masa rigakafin saida gwamnan ya yi rijistar amsar rigakafin a hukumance. Channels TV ta ruwaito

Dr. Ganduje ya yi kira ga al'ummar jihar da su bama jami'an lafiya haɗin kai wajen gudanar da rigakafin.

A jawabinsa, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Ibrahim Tsanyawa, ya godema gwamnan a kan gudummuwar da gwamnatinsa ke bayarwa wajen yaki da cutar.

"Ranka ya daɗe, muna matukar godiya da samar mana da duk abinda muke buƙata a fannin lafiya, muna jin dadin kyakkyawan shugabancinka musamman wajen yaƙi da yaɗuwar cutar COVID-19," Dr. Tsanyawa ya faɗa ma gwamnan.

Anyi ma Gwamna Ganduje Allurar rigakafin Korona A Asibitin Murtala dake Kano
Anyi ma Gwamna Ganduje Allurar rigakafin Korona A Asibitin Murtala dake Kano Credit: Ganduje TV
Source: Facebook

Kwamishinan ya bada tabbacin ma'aikatar sa a shirye suke su gudanar da rigakafin a faɗin jihar.

KARANTA ANAN: Mummunar cacar baki ta turnuke tsakanin Gwamnan Ribas da Jigon APC, Amaechi

"Kamar yadda ranka ya daɗe yayi rigakafin, hakan na nuni da cewa allurar mai inganci ce, kuma zata kare mutane daga kamuwa daga cutar Korona,"

Munason mutane su sani cewa, gwamnan mu a shirye yake ya shiga gaba akan kowanne lamari" inji Tsanyawa.

Yiwa gwamnan rigakafin yazo ne kwana biyu bayan taron da gwamnan ya yi da masu ruwa da tsaki a jihar, kamar Hukumar tsaro da kwararrun likitoci.

A lokacin taron, Gwamna Ganduje ya bayyana musu cewa gwamnatin sa zatayi duk me yuwu wa don ganin yaƙi da wannan cutar ya ƙarfafa.

Kasancewar Gwamnan ya yi rigakafin, na nuni da cewa an fara gudanar da ita a hukumance a jihar kano.

A wani labarin kuma An saki mutanen da ake zargi da haddasa rikicin Shasha, inda aka kashe Hausawa a Ibadan

Ran Hausawa ya baci kan sakin wadanda ake zargi da hadda rikici a kasuwar Shasha

Sakamakon haka masu kai kayan masarufi kudu suka shiga yajin aiki kafin suka janye.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Source: Legit

Online view pixel