An saki mutanen da ake zargi da haddasa rikicin Shasha, inda aka kashe Hausawa a Ibadan

An saki mutanen da ake zargi da haddasa rikicin Shasha, inda aka kashe Hausawa a Ibadan

- Ran Hausawa ya baci kan sakin wadanda ake zargi da hadda rikici a kasuwar Shasha

- An yi asarar rayuka da dukiya sakamakon wannan rikici

- Sakamakon haka masu kai kayan masarufi kudu suka shiga yajin aiki kafin suka janye

Sakamakon sakin mutane bakwai da ake zargi da haddasa rikicin kasuwar Shasha a garin Ibadan na jihar Oyo, wasu yan kasuwa sun nuna bacin ransu yayinda wasu ke kira ga a sake gudanar da bincike kan lamarin.

Wasu daga cikin yan kasuwan sun bukaci yan sanda su bayyana mutumin farko wanda shi ya kashe mai gyaran takalmi, wanda hakan ya haddasa kashe-kashe da lalace-lalacen dukiya.

Shugaban kungiyar yan kasuwan Shasha, Alhaji Usman Idris Yako, ya bayyana cewa al'ummar Hausa dake yankin basu ji dadin sakin wadannan mutane bakwai ba, Daily Trust ta ruwaito.

Yace: "Mun yi tunanin za'a hukuntasu ne domin haka ya zama darasi, amma ba ayi hakan ba."

"Ba muyi mamakin hakan ba, shi yasa muka ki komawa kasuwar Shasha. Mun koma kasuwancinmu a wani sabon wuri a Akinyele."

"Taimakon da gwamnati da wasu abokan arziki suka bada bai isa ba."

Ya kara da cewa an turo musu kayan tallafi ta hannun Sarkin Shasha wanda bai da wata alaka da kasuwar Shasha.

"Sarkin Sasa da bai da wata alaka da mu ya karbi yawancin kayan tallafin. Bai bamu komai ba. Mu abu ya shafa amma gamu nan shiru. Mun yanke shawaran ba zamu koma Sasa ba don kare rayukanmu," yace.

KU KARANTA: Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche

An saki mutanen da ake zargi da haddasa rikicin Shasha, inda aka kashe Hausawa a Ibadan
An saki mutanen da ake zargi da haddasa rikicin Shasha, inda aka kashe Hausawa a Ibadan Credit: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA NAN: Jerin jihohi 16 da suka samu kasonsu na rigakafin COVID-19 da adadin da suka samu

Amma, Cif Popoola Rasheed, Babaloja na kasuwar Sasa yace, "Ba zan so a dauresu ba tunda yan sanda da hukumar sun ce basu da laifi."

Kakakin hukumar yan sandan jihar Olugbenga Fadeyi, ya ce yan sandan sun sake su ne bisa umurnin Dirakta a ma'aikatar Shari'a.

"Sojoji ne suka kama mutane bakwan kuma suka mikasu hannun yan sanda. Mun fada muku cewa an sakesu ne bisa umurnin DPP," kakakin yace.

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi karin-haske a kan rikicin Yarbawa da Hausawa da aka yi a jihar Oyo.

Kamar yadda wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter ya nuna, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce ba duk kokarin da ya yi ne yake fito wa ya bayyana ba.

Ministan yake cewa ya yi magana da wadanda ya dace su duba kadin lamarin da kuma daukar hakki a kan wadanda aka zalunta a rigimar Shasha.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: