Mummunar cacar baki ta turnuke tsakanin Gwamnan Ribas da Jigon APC, Amaechi
- Rotimi Amaechi ya yi wa Nyesom Wike raddi kan wasu kalamai da ya yi
- Gwamna Nyesom Wike ya ce gwamnatin tarayya ce ke katange Ministan
- Ministan yayi magana, ya ce shi ya fi karfin ya kula tsohon yaran na sa
Da aka yi hira da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, a gidan talabijin na Arise TV, ya ce ba zai biye wa magajinsa, Nyesom Wike, da ya ke ta faman surutu ba.
Rotimi Amaechi, ya yi wa gwamnan jihar Ribas martani bayan ya zarge shi da batar da kudin al’ummar jihar Ribas, ya ce gwamnatin tarayya ta hana a kama shi.
A cewar gwamnan jam’iyyar adawar, Amaechi ya sace kudin al’umma a lokacin da yake mulki a jihar Ribas, duk da gwamnatinsu ta APC ta na ikirarin yaki da barna.
Ministan sufurin kasar ya kuma yi karin haske a game da maganar da ake yi na cewa ya kira gwamna Nyesom Wike da ‘dan-diya’, ya ce sam ba fa haka aka yi ba.
KU KARANTA: Amaechi ya yi magana a kan wanda zai gaji Buhari a 2023
“Ban ce haka ba, idan na yi haka, na ci mutuncin kujerar gwamna; cewa kurum na yi ba na yin magana a lokacin da na ke cikin maye.” Amaechi ya fayyace lamarin.
Amaechi yake cewa: “Ina tunani ba zan so in yi magana a kan gwamnan ba, na yi magana ta, na yi gaba. Tsohon ma’aikaci na ne, ni ba zan dawo da kai na kasa ba...”
“Na yi gwamna, na kuma yi shugaban majalisar dokoki, yanzu ni Minista ne. Sau biyu na rike kujerar shugaban gwamnoni. Me zai sa in yi magana a kan Wike?”
Da yake jawabi wajen kaddamar da ayyukan da gwamnatinsa ta yi, Wike ya bugi kirji ya na cewa ya koya wa Amaechi darasi a siyasa lokacin da aka gwabza a 2019.
KU KARANTA: Yemi Osinbajo ya fara yunkurin yi wa kusoshin APC sulhu a Imo
Wike ya kuma maida martani a kan zargin shan giya, ya ce babu laifi don mutum ya yi tatul, ya yi aiki.
Kwanaki aka ji cewa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da siyasantar da tallafin Naira biliyan 10 da aka ba jihar Legas.
Gwamnatin tarayya ta bada wannan makudan kudi ne domin yaki da cutar Coronavirus a Legas.
Gwamna Wike ya soki kokarin da gwamnatin Buhari ta ke yi na yaki da cutar COVID-19, yana mai cewa Buhari ya maida abin siyasa, a maimakon a kare lafiyar al'umma.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng