Abdulsalami da matarsa sun yi allurar riga-kafin COVID-19 a Minna

Abdulsalami da matarsa sun yi allurar riga-kafin COVID-19 a Minna

- Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulasalami Abubakar ya yi alluar rigakafin korona

- Mai dakinsa, Mai shari'a Fati Lami Abubakar ita ma ta karbi nata riga-kafin na COVID-19

- Abdulsalami da matarsa sun yi kira ga al'ummar jihar Niger da sauran yan Nigeria su rungumi rigakafin

An yi wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulasalami Abubakar da matarsa Mai shari'a Fati Lami Abubakar allurar riga-kafin korona a ranar Alhami 11 ga watan Maris, The Nation ta ruwaito.

An yi riga-kafin ne a gidan Abdulsalami da ke Uphill a Minna.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Manyan hafsoshin sojojin Nigeria sun dira garin Ibadan

Abdulsalami da matarsa sun yi allurar riga-kafin COVID-19 a Minna
Abdulsalami da matarsa sun yi allurar riga-kafin COVID-19 a Minna. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Bayan an masa riga-kafin, tsohon shugaban kasar na mulkin soja ya yi kira ga jama'ar jihar Niger su rungumi riga-kafin na COVID-19.

DUBA WANNAN: N2.5bn: Ban taɓa damfarar gwamnatin tarayya ba, in ji Zahra Buhari

Ya ce riga-kafin ne hanya daya da za a iya amfani da ita domin kawar da annobar daga kasar nan.

Matarsa, Mai shari'a Fati Lami Abubakar ta yi kira ga al'ummar jihar Niger da sauran yan Nigeria su dena shakku kan ingancin rigakafin inda ta kara da cewa rigakafin zai taimaka sosai wurin dakile yaduwa da kawo karshen kwayar cutar.

Gwamnonin jihohi da dama sun karbi allurar riga-kafin ta korona cikinsu akwai gwamnonin jihohin Kaduna, Kaduna da Jigawa.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel