Muhimman abubuwa 8 da su ka faru da Sanusi II bayan Gwamna Ganduje ya tsige shi daga sarauta

Muhimman abubuwa 8 da su ka faru da Sanusi II bayan Gwamna Ganduje ya tsige shi daga sarauta

- Yau shekara daya da aka tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

- Bayan kusan kwanaki 370 da barin sarauta nw ya samu halifancin Tijjaniya

- Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Ganduje ne ya tunbuke Malam Sanusi II

A rana irin ta yau ne a shekarar 2020, gwamnatin jihar Kano ta sauke Mai martaba Malam Muhammadu Sanusi II daga kan gadon sarautar gidan dabo.

Legit.ng Hausa ta tattaro rayuwar tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II bayan tunbuke shi a karagar mulkin Kano da ya shafe shekaru kusan shida a kai.

1. Maris, 2020 (Nasarawa)

Bayan an sauke Mai martaba Muhammadu Sanusi II, an wuce da shi zuwa wasu kauyuka a jihar Nasarawa, daga baya ya samu ‘yanci, ya wuce jihar Legas.

2. Maris, 2020 (KADIPA)

Jim kadan da sauke Muhammadu Sanusi daga sarauta sai gwamnatin jihar Kaduna ta nada shi a cikin masu kula da hukumar KADIPA mai jawo hannun jari.

KU KARANTA: Kwankwaso ya yi wa Ganduje raddi a kan tube Sanusi daga sarauta

3. Maris, 2020 (KASU)

Duk a cikin watan na Maris gwamnatin Nasir El-Rufai ta bakin Muyiwa Adekeye ta ce ta nada Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban jami’ar KASU.

4. Afrilu, 2020 (Madarij us salikeen)

A cikin watan Afrilun shekarar bara ne aka ji Muhammadu Sanusi II ya fara koyar da karatun addini ta kafar yanar gizo, ya dauki littafin Madarij us salikeen.

5. Agusta, 2020 (Sanagal)

Saboda alakar gidansu da Shaykh Ibrahim Inyass, a Agusta Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Sanagal inda ya yi ta’aziyyar wata rasuwa da aka yi a birnin Kaolack.

KU KARANTA: Muhammadu Sanusi II ya cika surutu, shiyasa na sauke shi - Ganduje

Muhimman abubuwa 7 da su ka faru da Sanusi II bayan Gwamna Ganduje ya tsige shi daga sarauta
Mai martaba Muhammadu Sanusi II Hoto: www.withinnigeria.com/news
Source: UGC

6. Satumba, 2020 (Oxford)

A Satumban shekarar bara ne Jami'ar Oxford ta Birtaniya ta zabi tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya fara karantar da dalibanta daga watan Oktoban 2020.

7. Fubrairu, 2021 (Kabara)

A watan Fubrairun bana ne Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi tir da da’awar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ya yi kira ga mutane su guji karantarwarsa.

8. Khalifan Tijjaniya

A ranar 13 ga watan Maris, 2021, aka nada Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifan Darikar Tijjaniya a Najeriya, ya gaji Marigayi Muhammad Sanusi II da ya rasu a 2018.

A 2020 tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da tunbuke masa rawani da gwamnatin jihar Kano ta yi, ya nuna ba zai kalubalanci matakin ba.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya nuna cewa a matsayinsa na musulmi, ya yi riko da kaddara, ya ce Ubangiji madaukaki ne ya ke bada mulki ga wanda ya so.

Sanusi II ya ke cewa daukaka ya ke nema ba mulki ba, kuma ya gode Allah da ya samu wannan.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit

Online view pixel