Tsohon Gwamna Kwankwaso ya yi wa Ganduje raddi a kan tube Sanusi daga sarauta

Tsohon Gwamna Kwankwaso ya yi wa Ganduje raddi a kan tube Sanusi daga sarauta

- Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana game da tsige Muhammadu Sanusi II

- Tsohon Gwamnan ya fitar da jawabi na musamman ya na yi wa Ganduje raddi

- Kwankwaso ya ce babu abin da ya hada Shugaba Jonathan da cire Sarkin Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya maida martani game da wasu kalamai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a kan tsige Sarkin Kano.

Tsohon gwamnan ya fitar da jawabin da ya yi wa take da ‘Ganduje and the blabbering of an imposter’ ta bakin babban sakatarensa, Malam Muhammad Inuwa Ali.

Ya ce: “Hankalin Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ga wani tarin karya da kokarin juya tarihi kuru-kuru da gwamnan Kano da aka kakaba, Abdullahi Ganduje ya fito ya yi.”

Jawabin ya ce: “Abdullahi Ganduje ya yi wannan magana ne wajen kaddamar da littafin daya daga cikin shugabanninmu masu daraja, Goodluck Ebele Jonathan GCFR.”

KU KARANTA: Ganduje: Kwankwaso ya na zargin sa hannun Buhari wajen tsige Sanusi

A ka’ida bai kamata kowa ya tanka mutum mai neman suna irin Ganduje ba, sai saboda cusa wasu ‘yan Najeriya masu daraja da ya yi, ya na neman ci masu mutunci.”

Muhammad Inuwa Ali a madadin Rabiu Kwankwaso ya fara da taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar rubuta littafi game da abin da ya faru da shi a mulki.

Kwankwaso ya ce: “Mun san cewa Ganduje ya na jin kan shi ba kowa ba a duk lokacin da yake tare da Sarkin, mun san cewa ya na da tsohuwar kiyayya da masarauta."

Tsohon gwamnan ya ce a dalilin haka ne gwamnatin Ganduje ta fara da Sarki Muhammadu Sanusi II, aka nada Sarakunan da za a su iya takawa gwamnatinsa burki ba.

KU KARANTA: Shehu Sani yana nemawa masu motoci a Kano alfarma wajen Ganduje

Tsohon Gwamna Kwankwaso ya yi wa Ganduje raddi a kan tube Sanusi daga sarauta
Tsohon Sarki Sanusi II Hoto: www.withinnigeria.com
Source: UGC

Sanata Kwankwaso ya kuma ambaci sukar cin bashin da gwamnatin Ganduje ta ke neman yi a wancan lokaci a matsayin abin da ya sa aka cirewa Sarkin na Kano rawani.

“Wannan shi ya kara sa aka tunbuke Sarki Sanusi II, babu abin da ya hada maganar da Jonathan.”

A kwanan nan baya kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta yi sababbin nade nade a masarautar karamar hukumar Karaye, kasar mahaifar tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

An nada Musa Saleh Kwankwaso, a matsayin 'dan majalisar nadin sarakuna a masarautar Karaye.

Wani jami'in gwamnati daga karamar hukumar Karaye ya bayyanawa 'yan jarida cewa sababbin wadanda aka yi wa nadin za su fara aiki a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel