Sanusi II: Riko da kaddara ce dalilina na yin tsit da aka tsige ni daga kan karagar mulki

Sanusi II: Riko da kaddara ce dalilina na yin tsit da aka tsige ni daga kan karagar mulki

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da tunbuke masa rawani da gwamnatin jihar Kano ta yi a farkon watan Maris, 2020.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya nuna cewa a matsayinsa na musulmi, ya yi riko da kaddara, ya ce Ubangiji madaukaki ne ya ke bada mulki ga duk wanda ya so.

Wannan jawabi na tsohon Sarkin ya na zuwa ne bayan kusan watanni shida da barin gadon mulki. Ya ce ya kafa tarihi a kasar Kano da ya gaji kakansa, abin da ba a taba yi ba.

Sanusi II ya fara da nuna godiya ga al’umma: “Mu na maraba da shehunnanmu, malamai, ‘yanuwa da abokanmu a kan zumunci da ku ka rike.”

Da ya ke magana da jaridar VOA, tsohon Sarkin ya kara da cewa: “Kamar yadda aka fada, mun samu albarkar zama da malamai.”

“Tun da mu ka bar Kano, ba mu tsaya mun yi magana a kai ba, babu amfanin maganar. Idan ana bin Al-kur’ani, an san abin da zai zo da abin da zai biyo baya in Allah ya so.”

Mai martaban ya ke cewa daukaka ake nema ba mulki ba, kuma ya gode Allah da ya samu wannan. Malam Sanusi II ya ce Allah madaukaki ne ya ke ba wanda ya so mulki.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Sultan Sa’ad Abubakar yayin da ya cika shekaru 64

Sanusi II: Riko da kaddara ce dalilina na yin tsit da aka tsige ni daga kan karagar mulki
Jama'a sun tarbi Sanusi II a Kaduna
Asali: Twitter

“Kwarai da gaske mun san yadda mutanen Kano da sauran yankin kasar nan su ke.” Inji Sanusi II game da sauke shi da aka yi daga karagar mulki bayan shekaru shida.

Mai martaban ya yi wannan jawabi ne a ziyarar da ya kawo jihar Kaduna a karshen makon jiya. Wannan ne karon farko da Sanusi II ya taka kafa a Arewa tun watan Maris.

Malam Sanusi II ya ke cewa sarauta rai ne da ita, kuma idan dai an yarda cewa Ubangiji ba ya zalunci sai a gode masa, a maimakon a yi fushi.

“Muddin ka duba ka ga cewa ba kai ka zalunci mutane, ko gwamnati ko ‘danuwanka ba, kai dai ba za a ce ga laifinka ba, sai ka godewa Allah.” Inji tsohon Sarkin.

Ya ce: “Duk wanda ya ce ya cire daga sarauta karya ya ke yi idan Allah bai kawo karshen ba, dama daga ranar da Allah ya rubuta za ka bar wuri, dole ka tafi ko a fitar da gawarka.”

Sanusi II ya na mai godiya ganin a cikin dubban zuriyar dabo shi ne Sarki na 12 a shekaru 200, wanda ko mahaifinsa bai yi Sarki ba, kuma shi ne jikan farko da ya yi mulki.

“Idan aka ce za ayi fushi, an yi wa Allah budulci, da bai bada ba fa? Da ya tashi karba, ran ka ya karba fa? Da yanzu ba a yi da kai.” Ya ce har ya mutu ya na godewa Allah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng