Siyasa Rigar 'Yanci, Jam'iyar APC ta cinye zaɓen cike gurbi a Jigawa

Siyasa Rigar 'Yanci, Jam'iyar APC ta cinye zaɓen cike gurbi a Jigawa

- Jam'iyyar (APC) dake mulkin ƙasar nan ta ƙara samun ɗan majilisar jiha a jihar Jigawa bayan sanar da sakamakon zaɓen cike gurbi a Kafinhausa

- Baturen zaɓen yankin Prof. Kutama ne ya bayyanar da sakamakon zaɓen bayan kammala tattarawa a ƙaramar hukumar Kafinhausa

- Baturen zaɓen ya bayyana Muhammad Adamu na (APC) a matsayin wanda yayi nasara

Jam'iyyar (APC) mai mulkin ƙasar nan ta cinye zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar jiha a Jigawa.

Ɗan takara a ƙarkashin jam'iyyar ta (APC), Muhammeɗ Adamu ne aka bayyana a matsayin zaɓaɓɓen ɗan majilisar jiha da zai wakilci mazaɓar Kafinhausa.

KARANTA ANAN: Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona

An gudanar da zaɓen cike gurbin na mazaɓar kafinhausan ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Adamu ya samu ƙuri'u 14,924 da suka bashi damar samun nasara akan sauran 'yan takarar na sauran jam'iyyu.

Kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito, An gudanar da zaɓen a rufunan zaɓe 120 dake faɗin mazabar ta Kafin Hausa.

Siyasa Rigar 'Yanci, Jam'iyar APC ta cinye zaɓen cike gurbi a Jigawa
Siyasa Rigar 'Yanci, Jam'iyar APC ta cinye zaɓen cike gurbi a Jigawa Hoto @APCnigeria
Asali: Twitter

Baturen zaɓen yankin, Prof. Ahmed Kutama, ne ya bayyana sakamakon zaɓen a runfar tattara sakamako dake karamar hukumar Kafinhausa, jihar Jigawa.

KARANTA ANAN: Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock

Yace ɗan takarar jam'iyar (APC), Muhammeɗ Adamu, ya samu nasara a kan abokin adawar sa, Garba Muhammad Tambale, na jam'iyyar PDP, wanda ya samu kuri'u 8,612.

Baturen zaɓen ya bayyana Muhammad Adamu na (APC) a matsayin wanda yayi nasara.

Mutum na uku da ya nemi kujerar ɗan majisar shine, Usman Isyako, na jsm'iyyar APM, wanda ya samu ƙuri'u 72 a zaɓen.

A wani labarin kuma Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna

Jami'an tsaro a Kaduna sun tabbatar da kashe akalla 'yan bindiga hudu a wani kwanton bauna da aka yi a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari na jihar

Gwamnan jihar Kaduna ya yabawa sojojin da namijin aikinsu na kawar bata-gari a yankin.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel