Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona

Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona

-Ko kusa najeriya ba zata kashe 10 biliyan ba wajen rarraba allurar rigakafin cutar corona kamar yadda mutane ke yadawa

-Shugaban hukumar lafiya ta ƙasa Dr. Faisal Shu'aib yace haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu ne suka ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.

-Ya tabbatar da cewa sun tanaji jirgi da kuma motar zirga-zirga da zasu yi aikin rarraba kayan zuwa jihohin kasar nan.

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton da wasu jaridun ƙasar nan suka ruwaito cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona zuwa jihohi.

Gwamnatin na shirye-shiryen raba rigakafin ta Astrazeneca guda 3.9 miliyan da aka kawo mata zuwa jihohi 36 na ƙasar nan da kuma babban birnin tarayya, Abuja.

KARANTA ANAN: Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta, Shugaban hukumar lafiya ta ƙasa, (NPHCDA), Dr. Faisal shu'aib, wanda ya zanta da 'yan jaridar gidan gwamnati ran asabar a Abuja, ya kira lamarin da shaci-fadi.

Ya bayyana cewa, haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu dake yaƙi da cutar corona, (CACOVID) ne zasu dauki nauyin raba rigakafin ba tare da sisin gwamnati yayi ciwo ba.

Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona
Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona Hoto: NCDCgov
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Shahararrun 'yan Najeriya 26 da suka mutu a wannan shekarar 2021

"Wannan bai dace ba, mun riga mun bayyana ma 'yan Najeriya cewa haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu dake yaki da cutar corona sun tanaji jirgi don aikin rabawa." Inji Dr. Faisal.

Yace jirgin zai tallafa matuƙa gaya wajen ɗaukar rigakafin daga Abuja zuwa jihohin da filin saukar jiragensu ke aiki.

Faisal yace "An tanadi motar ɗaukar kaya don ɗaukar rigakafin zuwa jihohin da filin jirginsu baya saukar jirgi."

Ni banga ta inda aikin zai lakume 10 biliyan ba, sabida haka labarin ba gaskiya bane" inji shugaban.

Gaskiyar itace abinda na faɗa muku a baya cewa: "(CACOVID) ne suka ɗauki nauyin raba allurar daga Abuja zuwa jihohin ƙasar."

"Abinda kawai nasan zamu kashe shine, ɗaukar rigakafin zuwa jihohin da filin jirginsu baya aiki, kuma wannan aikin bazai ci waɗannan maƙudan kuɗaɗen ba," A cewarsa.

A jawabinsa, Faisal yace gwamnati bazata kashe abinda yakai naira biliyan ɗaya ba wajen aikin.

A wani labarin kuma Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki

An dai kama jami'in sojan ne yana kai wa yan bindiga makamai da kayayyakin sojoji

Sai dai har zuwa yanzu hedkwatar tsaro bata ce uffam ba a kan batun.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel