Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock

Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock

- Fadar shugaba Buhari ta tabbatar da gobarar da ta auku a farfajiyar ASo Rock a ranar Asabar

- Kamar yadda Garba Shehu ya tabbatar, bangon fadar ta hanyar bariki zuwa Asokoro ne yayi gobarar

- Mai magana da yawun shugaban kasan ya tabbatar da cewa ba a rasa kadar ko rayuka ba yayin gobarar

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da tashin gobara a farfajiyar fadar shugaban kasa dake Aso Rock.

Kamar yadda Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasan ya sanar, lamarin ya faru ne tsakanin fadar da barikin sojoji kusa da hanyar Asokoro.

Ya musanta rade-radin da ake fadi na cewa gobarar a cikin fadar shugaban kasar ta tashi, The Cable ta wallafa.

A wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, Shehu yace wutar daji ce kuma ana cigaba da bincike a kan lamarin.

KU KARANTA: Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki

Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock
Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock
Asali: Original

"Jama'a a ciki da wajen kasar nan suna ta nuna damuwarsu a kan rahoton gobarar da ta tashi a Aso Rock, fadar shugaban kasan Najeriya. Ina son sanar da cewa ba a yi gobara ba a cikin fadar," Yace.

"Da yammaci ranar Asabar, 6 ga watan Maris, gobara ta tashi tsakanin bangon fadar shugaban kasa da barikin sojoji ta hanyar Asokoro.

“Kamar yadda ake tsammani, akwai yuwuwar masu wucewa ne suka yadda sigari. Hukumar kwana-kwana ta tarayya za ta bincika dalilin gobarar."

Amma kamar yadda Garba Shehu ya tabbatar, ba a rasa kadara ko rai ba.

KU KARANTA: Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya

A wani labari na daban, zakakuran sojin Najeriya sun sheke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan bindiga ne karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a Katsina, The Cable ta wallafa.

Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a ranar Alhamis a kauyen Marina dake karamar hukumar Safana ta jihar.

Akasin rahotannin da ke yawo na cewa an halaka sojoji masu yawa a yankin, Mohammed Yerima, kakakin rundunar sojin a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, yace soja daya ne ya rasa rayuwarsa a yayin musayar wutar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel