Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna

Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna

- Rundunar sojoji a jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga mutum hudu a wani yanki

- Kwamishinan tsaro na jihar ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar

- Gwamnan jihar Kaduna ya yabawa sojojin da namijin aikinsu na kawar bata-gari a yankin

Jami'an tsaro a Kaduna sun tabbatar da kashe akalla 'yan bindiga hudu a wani kwanton bauna da aka yi a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An kwato bindigogi uku da gatari daya daga hannun 'yan bindigar, wadanda suka kasance 'yan kungiyar ta'addancin da ke addabar sassan jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da kisan 'yan bindigan.

KU KARANTA: Kasar Autria ta dakatar da yin rigakafin Korona na AstraZeneca saboda zargin mutuwa

Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna
Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna Hoto: The Sun News
Source: UGC

A wata sanarwa, Aruwan ya ce bisa ga bayanin da suka samu daga rundunar Operation Thunder Strike (OPTS), an samu bayanan sirri kan 'yan bindigar da suka yi kaura daga kauyen Katika zuwa Antenna a karamar hukumar Chikun

Aruwan ya ce dangane da wannan, sojojin sun yi kwanton bauna a kauyen Antenna, kuma yayin da ‘yan bindigan suka matso, sai sojojin suka bude musu wuta, suka kashe hudu nan take a wurin.

Ya kara da cewa an kara fatattakar wasu 'yan bindigan a yayin samame ta sama da aka gudanar a kusa da kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari.

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yaba wa sojojin saboda matakin gaggawa da suka kai ga nasarar fatattakar ‘yan bindigar.

KU KARANTA: Yawan kabilu da addinai ke jawo kalubale wajen gina Najeriya, Osinbajo

A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun far wa unguwar ma'aikatan hukumar kula da filayen jirgin sama ta Najeriya (FAAN) da ke Jihar Kaduna, inda suka sace mutum 11.

Mai magana da yawun hukumar ta FAAN, Henrietta Yakubu, ta ce 'yan bindigan sun shiga unguwar ce da safiyar yau Asabar, kamar yadda ta shaida wa TheCable.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel