BUK ta sanar da ranar da zata fara jarabawar share fagen shiga Jami'ar

BUK ta sanar da ranar da zata fara jarabawar share fagen shiga Jami'ar

- Jami'ar Bayero dake jihar Kano (BUK) ta sanar da ran da za'a fara jarabawar share fagen shiga jami'ar (Post UTME).

- Mai kula da ɗaukar sabbin ɗalibai ce ta sanar da haka a wani saƙo da ta aikewa da manema labarai a Kano

- BUK tace an cire makafi da kurame a jerin waɗanda zasu zana jarabawar.

BUK ta sanar da ranar 18 zuwa 20 ga watan maris a matsayin ranar da zata gudanar da jarabawar share fagen shiga jami'ar wato (post UTME)

Mai kula da ɗaukar sabbin ɗalibai (registrar), Fatima-Binta Mohammed, ta bayyana haka a wani saƙo data aike wa manema labari ran Asabar.

KARANTA ANAN: Katin shaidar rigakafin korona zai zama sharaɗin fita daga Najeriya, in ji Boss Mustapha

Ta ce, zasu kulle neman izinin zana jarabawar a tsakiyar daren Jumu'a 12 ga watan maris.

BUK ta sanar da ranar da zata fara jarabawar share fagen shiga Jami'ar
BUK ta sanar da ranar da zata fara jarabawar share fagen shiga Jami'ar Hoto: @BUT_Nigeria
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kamata duk yan Najeriya su yi rigakafin korona

Bayan haka, ta bada umarni ga daliban da sukayi rijistar jarabawar da su sake fidda Slip ɗinsu don sanin ranar da zasu zana jarabawar daga ranar 15 zuwa 17 ga watan maris.

A wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, Fatima-Binta Mohammed tace, an cire makafi da kurabe a jerin waɗanda zasu zana jarabawar duk kuwa da cewa an yarda suyi rijista.

Ta ƙara da cewa: "Za'a bayyana ma kowane ɗalibi rana, lokaci da kuma wurin dazai zana jarabawar."

Hakanan kuma za'a turawa kowa ranar da zayyi jarabawar da wuri ta hanyar saƙon waya ta lambar da dalibin ya cike a JAMB.

Ta kuma kara bayyanar da cewa, za'a rufe yin rejistar tantacewa da ɗalibai keyi a shafin yanar gizo na makarantar a ranar 17 ga watan maris.

A wani labarin kuma Hayakin Janareta ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daliban jami'a 2

Rahotanni sun bayyana cewa, daliban sun mutu ne sakamakon kunna janareta yayin barci

Rundunar 'yan sanda na ci gaba da binciken lamarin, yayin da wani dalibin daban ke jinya a asibiti sakamakon shakar hayaki.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta Instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel