Hayakin Janareta ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daliban jami'a 2
- Rundunar 'yan sanda a jihar Imo ta tabbatar da mutuwar wasu daliban jami'a mutum 2
- Rahotanni sun bayyana cewa, daliban sun mutu ne sakamakon kunna janareta yayin barci
- Rundunar 'yan sanda na ci gaba da binciken lamarin, yayin da wani dalibin daban ke jinya a asibiti sakamakon shakar hayaki
Wasu daliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya dake Owerri (FUTO) biyu sun mutu bayan shakar hayakin janareta, Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro cewa daliban sun kunna janareta tare da fuskanto da hayakinsa zuwa tagogin dakin da suke kwana.
Kakakin rundunar 'yan sandar Jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, a wata sanarwa, ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin ne daga makwabtan daliban a Eziobodo, a yankin Ihiagwa dake Owerri ta yamma.
KU KARANTA: Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutune 11 a jihar Kaduna
Hedikwatar 'yan sanda ta bayyana cewa, dalibai uku ne ke kwana a wani dakin kwanan dalibai, wadanda suka hada da Nkama Fred Eberechukwu mai shekaru 22, Udeagbala Kenechukeu Enechukwu mai shekaru 21 da Anele Stephen mai shekaru 21, dukkansu kwance jina-jina.
“Jami’an sun kutsa kai cikin dakin kuma nan da nan aka kwashe su zuwa Asibitin tarayya dake Owerri, inda biyu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su Likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsu, amma Nkama ya yi nasarar farfadowa, kuma a halin yanzu yana jinya.
“Binciken farko ya nuna cewa wadanda lamarin ya rutsa da su da aka bayyana su daliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUTO) Owerri ne, mai yiwuwa sun mutu ne sakamakon hayakin (carbon monoxide) da ya fito daga janaretan, wanda suka shaka yayin barci.
"Amma, Kwamishinan 'yan sanda, na Jihar Imo, CP Nasiru Nasiru Mohammed, ya ba da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin, yayin da ake ci gaba da kokarin gano 'yan uwansu," in ji sanarwar.
KU LARANTA: Katin shaidar rigakafin korona zai zama sharaɗin fita daga Najeriya, in jiBoss Mustapha
A wani labarin, Shekarar 2021 ta kasance mai wahala ga Najeriya duk da cewa bata cika watanni uku ba. Wasu mashahuran 'yan Najeriya sun mutu sakamakon annobar COVID-19 yayin da wasu suka mutu sakamakon ajali ko rashin lafiya.
Jaridar The Nation ta hada rahoton fitattun mutane 26 da suka mutu daga farkon shekarar zuwa karshen watan Fabrairun 2021.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng