Katin shaidar rigakafin korona zai zama sharaɗin fita daga Najeriya, in jiBoss Mustapha
- Boss Mustapha ya bayyanawa 'yan Najeriya wajibcin yin allurar rigakafin cutar Korona
- Boss Mustapha yace da alamu nan gaba kadan allurar ta zama wajibi ga duk mai son fita wajen Najeriya
- Hakazalika ya bukaci 'yan Najeriya da su saki jiki da allurar da cewa tabbas bata da wata illa
Shugaban kwamitin yaki da kwayar cutar korona a Najeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum allurar rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya kasashen waje, BBC Hausa ta ruwaito.
Mustapha wanda kuma shi ne sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa a yau Asabar jim kadan bayan an yi wa shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo allurar rigakafin.
Ya bukaci 'yan Najeriya da su kokarta domin yin rigakafin da zimmar kare kansu daga cutar, wadda tuni ta halaka mutum kusan 2,000 a kasar da adadi mai yawa a sauran kasashen duniya.
KU KARANTA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna
"Yin dari-dari da allurar wajibi ne a daina shi domin kuwa maganar gaskiya ita ce, nan gaba kadan babu wanda zai fita daga kasar nan ba tare da ya nuna shaidar an yi masa ba," in ji Boss Mustapha.
"Ban tabbatar ba, amma na ji tuni wasu kasashe suka fara dakatar da karbar baki, ciki har da na ibada, idan ba su da shaidar rigakafin."
Ya kara da cewa Shugaba Mhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun gabatar da kansu ne a fara yi musu rigakafin domin su tabbatar wa da 'yan kasar cewa ba ta da wata illa.
KU KARANTA: Obasanjo: Na kamu da COVID-19 amma ban ji alamar komai ba a jikina har na warke
A wani labarin, A ranar Asabar ne aka yiwa Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) allurar rigakafin COVID-19, The Punch ta ruwaito.
Buhari ya yi rigakafin ne da misalin karfe 11.51 na safe a wani takaitaccen bikin da manyan jami’an gwamnati suka halarta a dakin taro na New Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.
Babban likitan kansa, Dr Shuaib Rafindadi Sanusi ne ya yiwa shugaban kasar allurar ta rigakafin, yayin da mataimakin shugaban kuma Dr Nicholas Odifre, likita na musamman ga mataimakin shugaban kasar, in ji jaridar The Nation.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng