Wasu jigogin APC a jihar Rivers sun fice daga jam'iyar bayan hukuncin kotu

Wasu jigogin APC a jihar Rivers sun fice daga jam'iyar bayan hukuncin kotu

- Ɓangaren shugaban riko Igo Aguma, ya fice daga jam'iyyar ta APC bayan kotu ta yanke hukunci

- Yace zasuyi ma hukuncin biyayya saidai bazasu cigaba da zama a jam'iyar da ba ta mutunta 'yayanta.

- Ya bayyana ficewarsa daga APC jim kadan bayan kotu ta bayyana ɗayan bangaren a matssyin shugaban riƙo

Ɓangaren shugaban jam'iyar APC a jihar rivers, Igo Aguma, da kuma wani jigo, Livingstone Wechie, sun fice daga jam'iyar.

Jigogin biyu sun bayyana ficewarsu ne jim kaɗan bayan kotun ƙoli ta bayyana, Isaac Ogbobula, a matsayin shugaban riƙo na jam'iyar reshen jihar ta Rivers.

KARANTA ANAN: Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano

Isaac Ogbobula, shine shugaban jam'iyya dake ɓangaren ministan tafiye-tafiye, Rotimi Amaechi.

Wasu jigogin APC a jihar Rivers sun fice daga Jam'iyar bayan hukuncin kotu
Wasu jigogin APC a jihar Rivers sun fice daga Jam'iyar bayan hukuncin kotu Hoto @ApcNigeria
Source: Twitter

KARANTA ANA: Tashin hankali: Sojoji sun harbe wani mutumi ɗan shekara 45 har lahira

Aguma da Wechie sun ce sun fice daga jam'iyar ne saboda gazawarta wajen samar da sahihin shugabanci a jihar.

A wani saƙo da Aguma ya fitar a babban birnin jihar yace, ya bar jam'iyyar ne saboda gazawarta wajen kare haƙƙoƙin 'yayanta.

"Naji hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na korar ƙarar dana shigar ina ƙalubalantar hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara tayi na ƙwace shugabancin riƙo daga wajena," a cewar Aguma.

A ɓangarensa kuma, Wechie, yace yana cikin kotun a lokacin da aka bayyana hukuncin kuma zai mutunta hukuncin.

A wani labarin kuma Jam’iyyar APC ta yi babban kamu na jigon PDP a jihar Yobe

Tsohon dan takarar na mataimakin Gwamnan PDP a zaben 2019 ya ce ci gaban da aka samu a karkashin Buni ne ya ja hankalinsa

Ya kuma sha alwashin bin tsarin jam’iyyar mai mulki yadda ya kamata

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram

@ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel