Jam’iyyar APC ta yi babban kamu na jigon PDP a jihar Yobe

Jam’iyyar APC ta yi babban kamu na jigon PDP a jihar Yobe

- Babban jigon jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Baba Abba-Aji ya sauya sheka zuwa APC

- Tsohon dan takarar na mataimakin Gwamnan PDP a zaben 2019 ya ce ci gaban da aka samu a karkashin Buni ne ya ja hankalinsa

- Ya kuma sha alwashin bin tsarin jam’iyyar mai mulki yadda ya kamata

Mista Baba Abba-Aji, dan takarar mataimakin gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Abba-Aji ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a wani biki da aka yi ranar Laraba a Damaturu.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

Jam’iyyar APC ta yi babban kamu na jigon PDP a jihar Yobe
Jam’iyyar APC ta yi babban kamu na jigon PDP a jihar Yobe
Asali: Facebook

Sakataren APC na jihar, Alhaji Abubakar Bakabe ne ya tarbe shi a wurin bikin wanda ya samu halartar Gwamna Mai Mala-Buni kuma Shugaban kwamitin kula da tsare-tsaren taron rikon kwarya na jam’iyyar .

Abba-Aji wanda ya sauya sheka tare da dubban magoya bayansa sun yi alkawarin bin tsarin mulkin APC.

Ya ce, ci gaban da Mala-Buni ya kawo ne ya ja hankalinsa zuwa ga jam'iyyar tare da iya daukar nauyin dukkan 'yan kasar, ba tare da la'akari da bambancin siyasa ba.

Bakabe ya baiwa wadanda suka sauya shekar tabbacin samun adalci a jam'iyyar a jihar.

KU KARANTA KUMA: NGF ta bayyana ranar da za'a yi ma gwamnoni allurar rigakafin corona

A wani labarin, 'Yan majalisar dokokin jihar Bauchi guda biyu sun fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sun koma Peoples Democratic Party, PDP a jihar, rahoton The Punch.

Mai magana da yawun kakakin majalisar dokokin jihar ta Bauchi, Abdul Burra ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Laraba kuma ya raba wa manema labarai sanarwar.

Mambobin majalisar sune Yusuf Bako mai wakiltar mazabar Pali da Umar Yakubu mai wakiltar mazabar Udubo.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel