Tashin hankali: Sojoji sun harbe wani mutumi ɗan shekara 45 har lahira

Tashin hankali: Sojoji sun harbe wani mutumi ɗan shekara 45 har lahira

- Sojoji sun harbe mutumin ne bayan wata ƴar taƙaddama data barke a yayin da suka biyo wani direban mota

- Shaidun da lamarin ya auku a gabansu sun tabbatar da kisan mutumin ɗan shekara 45

- Magajin garin yace suna tattaunawa da sojojin dan ganin andawo da zaman lafiya a yankin

An samu tashin hankali a yankin Assa, dake Jihar Imo, bayan wasu sojoji sun kashe wani Mutumi Ɗan shekara 45

Sojojin sun biyo wani mutumi ne da suke zargin barawan man fetur ne.

Barawon wanda akafi sani da suna "asari" na ƙoƙarin guduwa ne a wata motar daukar man fetur.

Lamarin ya auku ne a kasuwar Afor Assa, a ran laraba da daddare.

Yan kauye sun shiga ɗimuwa da kuma tsoron kar wani harsashi yazo ya samesu.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Shugaban Majalisa ya ce manyan dillalan miyagun ƙwayoyi ke ɗaukan nauyin ƴan bindiga

A rahoton da Thenation ta wallafa, matasan sun tare motar dake dauke da man petur wanda ake tsammanin sojojin sun biyo motar ne.

Wani da lamarin ya auku a gabansa, yace: "Matasan sun bukaci a basu direban motar ya biyasu kafin subari ta cigaba da tafiya."

Tashin hankali: Sojoji sun harbe wani mutumi ɗan shekara 45 har lahira
Tashin hankali: Sojoji sun harbe wani mutumi ɗan shekara 45 har lahira Hoto @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji

"Kawai sai sojojin suka shiga lamarin kuma suka hana mai motar ya ba wani matashi ko sisi, Har takai ga an kasa shawo kan lamarin." a cewar mai idon shaida

"Domin tsoratar da matasan, Sai sojojin suka fara harbi a sama." a faɗarsa.

Daya daga cikin harsashin ne ya sami mutumin, wanda hakan yasa ya rasa ransa.

A binciken da wani ma'aikacin TheNation yayi, ya gano cewa wani harsashi ya sami wani matashi amma anyi gaggawar kaishi asibiti domin duba lafiyarsa.

Wani shaidan da ya gane ma idonsa lamarin yace "Bayan harbin, mutumin ya mutu nan take, sojojin sun kama direban motar Asari suka tafi dashi."

Matasan yankin sun ƙona motar gaba ɗaya.

Magajin garin Assa, Eze Emmanuel Assor, Yace suna tattaunawa da shuwagabannin sojoji don tabbatar da zaman lafiya a garinsa.

Ya ƙara da cewa "Muna tattaunawa da sojoji, munason mudawo da zaman lafiya mai ɗorewa yankin mu Kuma bama fatan haka ta sake faruwa anan gaba"

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun sojojin yankin yace: "Banda labarin abinda ya faru saboda ina hutu"

Sai dai mai maganna da yawun yan sandan jihar Imo ya tabbatar da kisan, ya kuma tabbatar da cews ƴan sanda sunje wajen don dawo da zaman lafiya.

A wani labarin kuma An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalissar Wakilai Ta Jihar Imo

Kakakin majalisar wakilai ta jihar Imo ya bayyana tsige shugaban masu rinjaye na majalisar a yau Alhamis.

Uche Ogbuagu ya rasa mukaminsa ne bayan kada kuri'a da mafi yawan wakilan sukayi.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel