Shugaban Majalisa ya ce manyan dillalan miyagun ƙwayoyi ke ɗaukan nauyin ƴan bindiga

Shugaban Majalisa ya ce manyan dillalan miyagun ƙwayoyi ke ɗaukan nauyin ƴan bindiga

- Shugaba Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci a sauya tsarin NDLEA don rage yawan masu sayar da miyagun kwayoyi

- Lawan ya bayyana wannan bukatar ne yayin da yake jawabi lokacin da Buba Marwa, shugaban NDLEA ya kai masa ziyara ranar Alhamis

- Lawan ya bukaci a kara wa NDLEA karfi kamar yadda hukumomi irinsu EFCC da ICPC suke don kawo karshen ta'addanci a kasarnan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi jawabi lokacin da shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa ya kai masa ziyara majalisar a ranar Alhamis, rahoton The Cable,

A wata takarda wacce hadimin shugaban majalisar dattawa na musamman, Ezrel Tabiowo ya saki, ya bayyana inda Lawan yace masu sayar da miyagun kwayoyi sun baje kolinsu a Najeriya.

Tsaro: Masu safarar miyagun kwayoyi ke daukan nauyin ta'addanci, Shugaban Majalisa, Lawan
Tsaro: Masu safarar miyagun kwayoyi ke daukan nauyin ta'addanci, Shugaban Majalisa, Lawan. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Lawan ya bukaci a sauya tsarin NDLEA, a kara wa hukumar karfi don kawo karshen siye da siyar da miyagun kwayoyi a kasarnan.

A cewarsa, majalisar dattawa zata bayar da gudun mawa kwarai wurin kawo gyara ga hukumar NDLEA.

"Na yarda da cewa ya kamata a gyara hukumar nan. Yanzu da ka hau wannan kujera, ya kamata mu hada karfi da karfe wurin kawo gyara, don hakan ya kamata ayi a halin yanzu," a cewar Lawan.

"A shawarace, ya kamata NDLEA ta samu karfi da matsayi kamar yadda hukumomi irin EFCC da ICPC suke dasu, don hakan zai bata damar gudanar da ayyukanta yadda ya dace.

"Don haka tabbas majalisar dattawa zatayi aiki da ku, zamu hada kai kuma mu tabbatar munyi iyakar kokarinmu don ku kawo gyara a kasarnan.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

"Yanzu haka masu sana'ar miyagun kwayoyi sun baje kolinsu a Najeriya. Suna harkokinsu yadda suka ga dama a kasarnan.

"Wajibi ne a dakatar da hakan don su ne suke daukar nauyin ta'addanci, shiyasa 'yan ta'adda suke da miyagun makamai.

"Tabbas wannan aikin masu sana'ar miyagun kwayoyi ne, ba 'yan ta'adda ba.

"Don haka wajibi ne a dakatar da harkokin miyagun kwayoyi a kasarnan ta hanyar bincike da jajircewar hukumomi kamar na kwastam, hukumar shige da fice, jami'an tsaro har da FAAN da hukumar dake tsare bakin ruwa."

Lawan ya kara nuna muhimmancin hada kai da duk jami'an tsaron gwamnati don kawo karshen rashin tsaro, karancin ilimi, rashin ayyukan yi da fatara.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel