Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji

Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji

- Rundunar sojojin Nigeria ta karyata rahoton da aka wallafa na cewa dakarunta 100 sun tsere bayan harin Boko Haram

- Rundunar sojojin ta ce labarin ba gaskiya bane kuma wasu da ke nufin bata mata suna ne suka kirkire shi da nufin karya gwiwar sojoji

- Kakakin sojoji, Janar Mohammed Yerima ya ce an samu tsaikon sadarwa yayin kidayya sojojin bayan harin amma daga bisani an gano sojojin kuma suna cigaba da aikinsu

Rundunar sojojin Nigeria ta karyata rahoton cewa wasu jami'anta da sojoji sun tsere daga wurin aikinsu bayan harin da Boko Haram ta kai Marte da Dikwa a jihar Borno, The Nation ta ruwaito.

A cewarta labarin ba shi da tushe ballantana makama kuma da ake neman amfani da shi don bata wa rundunar suna.

Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji
Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abdul-Jabbar: JNI ta ce ba za ta hallarci muqalabar da gwamnatin Kano ta shirya ba

Kakakin rundunar soji Janar Mohammed Yerima cikin wata sanarwa ya ce an samu matsalar sadarwa na cikin gida.

Ya ce: "An janyo hankalin rundunar soji kan wani rahoto da aka wallafa a wasu kafafen watsa labarai na cewa fiye da sojojin Nigeria 100 sun bar wurin aikinsu bayan harin da Boko Haram ta kai Marte da Dikwa.

"Rahoton ba gaskiya bane, kuma ba shi da tushe ballantana makama kuma yunkuri ne na bata sunan rundunar sojojin Nigeria.

KU KARANTA: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

"Al'addar soji na a lokacin yaki ta kidiyaa dakarunta da makamansu bayan an kai hari.

"Sai dai, an samu kuskure wurin kidaya wannan karon. Daga baya an gano wadanda abin ya shafa da dama sun koma wurin aikinsu kuma a yanzu suna cigaba da yaki da yan ta'addan."

Rundunar sojin ta bukaci jama'a su yi watsi da rahoton domin wasu ne da ke neman karya lagwan sojoji ke kirkirar irin wannan labaran.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel