An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalissar Wakilai Ta Jihar Imo

An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalissar Wakilai Ta Jihar Imo

- Kakakin majalisar wakilai ta jihar Imo ya bayyana tsige shugaban masu rinjaye na majalisar a yau Alhamis.

- Uche Ogbuagu ya rasa mukaminsa ne bayan kada kuri'a da mafi yawan wakilan sukayi.

- Ya zama dan majalisar ne a karkashin jam'iyyar PDP amma daga bisani ya sauya sheka zuwa APC

Hatsaniyar rikicin siyasar data turnuke majalissar jihar Imo tayi tsamari inda ta kai ga tsige shugaban masu rinjaye na majalissar, Uche Ogbuagu a ran Alhamis.

An tsige shi ne a zaman da majalissar ta gudanar yau Alhamis, inda mafiya yawan yan majalissar suka goyi bayan a tsige shi.

KARANTA ANAN: 'Yan majisar jiha biyu Sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Zaman majalisar na yau ya gudana ne cikin matsanancin tsaro.

Kakakin majalissar Paul Emizem ne ya sanar da batun tsigewar.

Ogbuagu dan majalissa ne dake wakiltar ƙaramar hukumar Ikeduru dake jihar ta Imo.

An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalissar Wakilai Ta Jihar Imo
An Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalissar Wakilai Ta Jihar Imo Hoto: @GovtofImoState
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Wasu shugabannin APC na yiwa Bola Tinibu zagon kasa

An zaɓe shine a ƙarƙashin jam'iyyar PDP inda daga bisani ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Ya sauya sheƙar ne biyo bayan cire Emeka Ihedioha, wato tsohon gwamnan Imo da wata kotu tayi a watan Janairun shekarar 2020.

Domin ya samu damar zama cikin masu gudanarwa na majalissar.

A wani labarin kuma, Kungiyar Ibo ta maidawa ‘Yan Arewa martani, ta ce za mu fara noma abincin da ku ke takama da shi

Mutanen Ibo ta bakin Alex Ogbonnia, sun ce noma za su fara babu kaukautawa

A ranar Laraba, 3 ga watan Maris, 2021, kungiyar kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo, ta ce hana shigo da abinci da wasu kungiyoyin Arewa su kayi ba zai taba su ba.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel