Tsohon dan takarar shugaban kasa, Shittu, ya koma jam'iyyar APC

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Shittu, ya koma jam'iyyar APC

- Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin rusasshiyar jam’iyyar Advanced People’s Democratic Alliance (APDA), Alhaji Mohammed Shittu, ya sauya sheka zuwa APC

- Shittu ya yi kira ga tsarin kafa jam'iyyu biyu a kasar don karfafa dimokuradiyya da zamantakewar kasar

- Ya kuma sha alwashin cewar za su karfafa tattalin arziki da zaman lafiyar kasar ta ajandar APC

Wani tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin rusasshiyar jam’iyyar Advanced People’s Democratic Alliance (APDA), Alhaji Mohammed Shittu, ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

APDA ta kasance daya daga cikin jam’iyyun siyasa 74 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta soke wa rajista a shekarar 2020.

Shittu, tsohon shugaban jam’iyyar APDA na kasa, wanda ya yi rajista a shiyyarsa ta Gwagwa da ke babban birnin tarayya Abuja, ya yi kira da a kafa tsarin jam’iyyu biyu a kasar.

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Shittu, ya koma jam'iyyar APC
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Shittu, ya koma jam'iyyar APC Hoto: Leadership.ng
Asali: UGC

Ya fada wa manema labarai cewa tsarin jam’iyyu biyu, idan aka amince da shi, zai taimaka wajen gina dimokuradiyya mai karfi da bunkasa rayuwar zamantakewar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

“Daga yau, za mu shiga ne domin kafa jam’iyyar siyasa mai karfi wacce za ta gina tattalin arziki mai karfi da kuma zaman lafiyar kasar.

“Ina kira ga‘ yan Najeriya da cewa yanzu ya kamata a kafa tsarin jam’iyyu biyu a cikin kundin tsarin mulkin mu domin mu gina kasa mai karfi.

“Don ci gaban wannan kasar, dole ne jam’iyyun siyasa su hadu wuri daya.

“Don haka, mun yanke shawara a yau cewa za mu hade da APC don gina ƙasa mai ƙarfi.

"APC ta kawo ajandar kawo canji kuma yanzu mun yi imanin cewa lokaci ya yi da dole ne rundunonin da ke son kasar nan ta ci gaba su hade," in ji Shitu.

KU KARANTA KUMA: Idan da Sheikh Gumi Kirista ne, da gwamnatin Buhari ta yi Allah wadai da kalamansa, sannan ta kame shi, CAN

Shittu, tsohon Shugaban Jam’iyyar APDA na kasa, ya samu rakiyar tsohon dan takarar shugaban kasa na rusasshiyar United Progressive Party (UPP), Cif Chekwas Okorie, wanda shi ma ya koma APC kwanan nan.

A wani labarin, Jam'iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta kori Aminu Ibrahim, ɗan takarar ta na gwamna a zaɓukan 2015 da 2019 da suka gabata bisa tuhumar sa da cin amanar jam'iyyar.

Wannan mataki dai yana da alaƙa da saɓanin da shi Aminu Ibrahim ɗin ya samu da tsohon gwamnan jahar wato Sule Lamido wanda Aminun yayi wa shugaban ma'aikata a lokacin da yake kan karagar mulki.

Premium times ta ruwaito cewa a ranar Laraba shugaban jam'iyyar PDP na jihar ta jigawa wato Ibrahim Babandi ya bayyana cewa yan majalissun ƙoli na jam'iƴƴar suka yanke hukuncin korar Ibrahim ɗin.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel