Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

- Tubabbun 'yan bindiga uku da suka rungumi zaman lafiya a Zamfara sun ce sunyi hakan ne domin ra'ayinsu da kuma son zaman lafiya

- Yan bindigan sun ce sun yi nazari sun gano cewa gwamnatin Matawalle ba yaudara ta ke yi ba kuma da gaske zaman lafiya da adalci ta ke so

- A bangarensa, Gwamna Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da daukan duk matakin da ya dace don samun zaman lafiya a jihar

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a jiharsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tarbar tubabbun yan bindiga uku da suka mika AK-47 dinsu da wasu makamai a gidan gwamnati a Gusau, The Nation ta ruwaito.

Abin da yasa muka tuba muka mika makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara
Abin da yasa muka tuba muka mika makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

Tubabbun yan bindigan da suke fashi a karamar hukumar Bakura na jihar sun ce sun rungumi tsarin zaman lafiya da sulhu na jihar ne domin ra'ayin kansu kuma domin samun zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da sulhu da karbar makamai domin ganin an samu zaman lafiya a jihar ta inda kowa zai yi rayuwarsa ba tare da tsoro ba.

Ya ce sulhu ne kadai sai magance matsalar rashin tsaron da ke damun jihar da ma kasa baki daya. Gwamnan ya ce babu karfin bindiga baya kawo karshen rikici ko yaki.

Ya kuma yi kira ga jama'ar jihar su taimakawa gwamnatinsa wurin ganin zaman lafiyar da ake samu ya dore a kokarin da ya ke yi na kawar da ayyukan bata gari.

KU KARANTA: Za mu bar yaran Kagara da yunwa har su mutu, in ji mai garkuwa

Ya kuma jinjinawa jami'an tsaro a jihar saboda gudanar da ayyukansu yadda ya dace. Ya tabbatar musu gwamnatinsa za ta cigaba da basu hadin kai da goyon baya.

Shugaban tubabun yan bindigan, Amadu Katare ya ce sun yanke shawarar ajiye makamansu ne saboda yadda gwamnan ya nuna tsakani da Allah ya ke so a yi sulhun da neman zaman lafiya.

Ya ce tun zuwar gwamnatin Matawalle da bullo da tsarin sulhun sunyi nazari don ganin ko yaudara ce kamar yadda ake yi a baya amma sun gano gwamnan yana son yi wa kowa adalci.

Amadu ya ce kashe iyayensa, yaransa da matansa da yan sa-kai suka yi ne yasa ya shiga kungiyar yan bindiga.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel