Allah ya yi wa sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya rasuwa a Kwara

Allah ya yi wa sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya rasuwa a Kwara

- Babban sarki mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya rasu

- Basarken ya rasu ne a daren ranar Lahadi 21 ga watan Fabarairun shekarar 2021 bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya

- Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya mika sakon ta'aziyya ga jama'ar masarautar tare da addu'ar Allah ya jikan sarkin

Basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Allah ya yi wa sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya rasuwa a Kwara
Allah ya yi wa sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya rasuwa a Kwara. Hoto: The Nation News
Source: Twitter

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Mai girma gwamna ya ce ya yi bakin cikin samun labarin rasuwar Mai martaba Olupo na Ajase-Ipo a daren ranar Lahadi.

"Olupo mutum mai daraja, mai son jama'arsa, sarki da ya dace a yi koyi da shi wanda masarautarsa ta bunkasa a karkashin mulkinsa. Son zaman lafiya da hadin kai da cigaba shine dalilin da yasa ake matukar kaunar basaraken," a cewar gwamnan cikin sakon da sakataren watsa labaransa Rafiu Ajakaye ya fitar.

Gwamna ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya kuma bawa masarautarsa hakurin jure rashinsa.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel