Za mu bar yaran Kagara da yunwa har su mutu, in ji mai garkuwa
Wadanda suka sace dalibai 27 da ma'aikata 15 na Kwallejin Gwamnatin Kimiyya ta Kagara a jihar Niger, sun yi barazanar cewa za su hora su da yunwa har su mutu idan ba a biya su kudin da suke nema a kan lokaci ba.
Daya daga cikin wadanda suka sace yaran ne ya bayyana hakan cikin wani magana da aka nada da wakilin The Punch ya samu a ranar Laraba daga hannun Sheikh Ahmad Gumi.
DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya
A cikin muryar da aka nada, an ji daya daga masu garkuwar, yana magana da harshen Hausa tare da wani da Gumi ya ce daya daga cikin manyan jami'an makarantar ne.
Ya ki amincewa da Naira miliyan 2.7 da aka ba shi a matsayin kudin fansa domin ceto wadanda aka yi garkuwar 27.
Dan bindigan ya ce, "Ba ni da abincin da zan basu. Duk wanda ya mutu cikinsu, zan fada muku inda za ku tafi ku dauki gawar.
"Ka san yaran nan suna jin yunwa. Ba ni da abincin da zan basu, ruwa ne kawai kuma idan za su mutu, sai dai su mutun."
Mai magana da mai garkuwar ya ce zai yi wahala ya samu lambar wayoyin dukkan iyayen yaran kamar yadda mai garkuwar ya bukata.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna
Mai garkuwar ya mayar masa da cewa ya san dukkan jami'an tsaron da aka turo Kagara, inda ya rantse cewa ba za su iya ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba.
"Kana tunanin ban san bin abinda kuke yi bane? Ina iya fada maka adadin motocin jami'an tsaro da ke Kagara a yanzu da muke magana.
"Da taimakon yan gari akan ci gari. Ko baka san hakan ba? Wanda ya bamu wannan kwangilar yana cikinku. Yana nan tare da ku duk inda kuke zuwa, yana kallon ku. Idan za ka yi abinda ya dace kayi. Daga Allah muke kuma wurinsa za mu koma.
"Ko ka tattaro dukkan jami'an tsaron Nigeria sun zo Kagara, ina da ido a ko ina. Duk matakin da zaka dauka a Nigeria, wallahi, zan sani. Kuna cewa kada a biya, idan an biya mu, za mu yi amfani da kudin mu siya makamai. Da wane kudin muka siya makaman mu? Idan ba mu da makamai, za ku turo jami'an tsaro ne kawai su kashe mu su dauki yaran," a cewarsa.
Da ya ke rokon mai garkuwar, mai neman sulhun ya ce, "Iyayen yaran sun amince za su biya Miliyan 2.7, kowannensu zai biya N100,000."
Ammai mai garkuwar bai yarda ba inda ya yi barazanar zai fitini garin Kagara, inda ya ce ya bar wa yaransa wasiyya ko ya mutu kada su bari a samu zaman lafiya a Kagara idan aka kashe shi.
Ya kuma soki gwamnonin da suke cewa kada a biya su kudin fansa.
A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.
Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng