Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya
- Wata dattijuwa mai shekaru 91 ta auri masoyinta mai shekaru 73 a kasar Jamaica
- Masoyan sun yanke shawarar yin aure ne bayan yin soyayya na fiye da shekaru 10
- Soyayyarsu ta samu asali ne tun 2009 lokacin da matar ta yi rashin lafiya mijin kuma ya yi jinyarta har da warke
Wata mata mai shekaru 91 a duniya ta auri sahibinta, wani mutum mai shekaru 73 bayan shafe shekaru fiye da 10 suna soyayya, rahoton jaridar The Nation.
An kuma gwangwaje biki na kece raini a ranar daurin auren na su.
DUBA WANNAN: 'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC
Matar mai suna Evelina Meadder ta auri saurayinta da suka dade tare mai suna Calgent Wilson mai shekaru 73 a wani babban biki da aka shirya a kasar Jamaica.
A cewar rahoton da The Mirror ta wallafa, ma'auratan sun fara soyayya ne tun a shekarar 2009 a lokacin da Evelina ta kamu da rashin lafiya, shi kuma Calgent, manomi, ya yi jinyarta har zuwa lokacin da ta warke.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna
Evelina ta ce sun daga lokacin suka shaku, ya kan mata maganar cewa ya kamata su yi aure amma a lokacin da ya ke shan barasa ne sai kawai ta yi dariya ta yi watsi da zancen.
Daga karshe dai sun yi auren kuma muna musu fatan alheri.
A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.
Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng