2023: Hadimin Tsohon Shugaban kasa ya karyata rade-radin takara da komawar Jonathan APC

2023: Hadimin Tsohon Shugaban kasa ya karyata rade-radin takara da komawar Jonathan APC

- Reno Omokri ya karyata rade-radin barin Dr. Goodluck Jonathan Jam’iyyar PDP

- Fasto Reno Omokri ya ce tsohon shugaban Najeriyar bai da niyyar takara a 2023

- Hadimin tsohon shugaban kasar ya yi watsi da rahoton takara da Nasir El-Rufai

Tsohon hadimin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce mai gidansa ba zai taba yin takara tare da Gwamna Nasir El-Rufai ba.

Ana rade-radin cewa tsohon shugaban kasar zai tsaya takara da Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa a zabe mai zuwa na 2023.

Jaridar Punch ta rahoto Reno Omokri ya na cewa Goodluck Jonathan bai da niyyar sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, ko kuma ya nemi shugaban kasa.

Reno Omokri ya yi wannan bayani ne da aka yi hira da shi a wani shiri da ake kira The Roundtable.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya yi magana game da rade-radin barin PDP

Omokri wanda ya yi aiki a matsayin mai ba Goodluck Jonathan shawara a lokacin da yake mulki ya ce duk jita-jitar komawar Jonathan APC ba gaskiya ba ne.

“Su na yada wannan labari ne saboda su saida Nasir El-Rufai a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa.”

“Na yi magana da Jonathan kafin wannan hirar. Labarin nan karya ne, ku ce ni ne na fada. Nasir El-Rufai ne mutumin karshe da Jonathan zai yi takara da shi.”

Ya ce: 'Idan ma har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya na da niyyar yin takara kenan, kuma ko tunanin ya tsaya neman kujerar shugaban kasa ba ya yi.”

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa 12 da su ka bar Jam’iyyarsu, su ka tafi APC

2023: Hadimin Tsohon Shugaban kasa ya karyata rade-radin takara da komawar Jonathan APC
Reno Omokri Hoto: @renoomokri
Asali: Instagram

“Iyaka sani na Jonathan ba zai canza sheka ba. Jam’iyya guda kadai ya taba yi, shekararsa 63, kuma bai da tarihin canza jam’iyya. Mutum ne shi mai amana, iri na.”

Kwanaki kun ji tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi bayani a kan batun tsayawa takara a 2023, hakan na zuwa ne bayan rade-radin da ake ji.

A cewarsa, ya yi wuri ya fara bayyana ra'ayinsa na tsaya wa takarar shugaban kasa. Ya ce ya kamata a maida hankula a kan wasu matsalolin da ke addabar kasar.

Rahotanni sun ce akwai wasu gwamnonin APC huɗu sda su ka matsa wajen zawarcin Jonathan.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel