2023: Jonathan ya yi martani a kan batun tsayawarsa takara
- Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi bayani a kan batun tsayawa takara a 2023
- Ya ce ya kamata a mayar da hankula a kan wasu matsalolin da ke addabar kasa a halin yanzu
- A cewarsa, ya yi wuri ya fara bayyana ra'ayinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023
Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya, yayi magana a kan yuwuwar kara tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Jonathan ya ce ya yi wuri, batun fara bayyana burinsa na tsayawa takara a 2023.
Legit.ng ta ruwaito yadda tsohon shugaban kasan, a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba, bayan kammala wani taro da Commonwealth Community Choir ta shirya a Abuja, yace akwai sauran matsaloli da yakamata hankula su karkata, ba na zabe ba.
A cewarsa, ya yi wuri a ce ya fara bayyana burinsa na tsayawa takarar shugabancin 2023.
KU KARANTA: Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari
KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta matukar girgiza da kalubalen tsaro, Gwamnoni
A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce sai an zage damtse kafin a samu nasarar yaki da 'yan ta'adda a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
A jiya ne Tinubu ya nuna matsananciyar damuwarsa a kan yadda 'yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 na jihar Borno kisan wulakanci.
Manoman da basu ji ba basu gani ba, sun mayar da hankulansu wurin nema wa iyalansu abinci, amma rashin tsaro ya janyo musu bala'i.
Ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Gwamna Babagana Zulum da daukacin jama'ar jihar Borno a kan kisan monoman kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar.
Ya sanar da hakan ne a wata takarda wacce ya aika wa gwamnan kuma ofishin harkokin yada labaran Tinubu suka bayyana wa manema labarai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng